Ramadan 1445: Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Matakin Saukakawa Ma’aikata da Azumi

Ramadan 1445: Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Matakin Saukakawa Ma’aikata da Azumi

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki mataki na saukaka wa ma'aikatan gwamnatin jihar a wannan lokaci na azumin watan Ramadan
  • Gwamnan jihar, Umar Namadi ya amince da rage awanni biyu daga lokutan aikin, inda za a fara karfe 9:00 na safe a tashi karfe 3:00 na rana
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani ma'aikaci a jihar Jigawa, kan wannan mataki na rage lokacin zuwa aiki da gwamnan ya yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya amince da rage awanni biyu daga lokutan aiki a jihar yayin da aka fara azumin watan Ramadan na shekarar 1445.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Muhammad K. Dagaceri.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito

Gwamnan jihar Jigawa ya rage lokutan zuwa aiki
Gwamnan Jigawa ya rage awanni biyu a lokutan aiki ga ma'aikatan jihar. Hoto: @uanamadi
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce a yanzu ma’aikatan jihar za su je ofis da karfe 9:00 na safe kuma za su tashi da karfe 3:00 na rana tsakanin Litinin zuwa Alhamis maimakon karfe biyar na yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bugu da ƙari, ma'aikata za su je aiki a ranar Juma'a da ƙarfe 9:00 na safe kuma su tashi da ƙarfe 1:00 na rana kamar yadda aka saba."

-A cewar sanarwar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Manufar rage lokutan aiki a Jigawa

Ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne da nufin samar da karin damammaki ga ma’aikatan jihar domin su samu nutsuwa da yalwar lokaci na yin ibada a Ramadan.

Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, ana fatan ma’aikatan jihar za su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen yi wa jihar addu’ar neman kariya da kuma albarkar Allah SWT.

Kara karanta wannan

Matatar man Fatakwal za ta fara aiki yayin da Najeriya ke shirin daina shigo da fetur

"Har ila yau, ana fatan ma'aikatan gwamnati za suyi amfani da lokacin azumi domin yin addu'a ta samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar da Najeriya baki daya".

- A cewar Dagaceri.

"Gwamna Namadi ya san darajar ma'aikata" - Nasir

Wani ma'aikaci a jihar Jigawa, Nasir Muhammad Dikko, ya zanta da Legit Hausa a shafin WhatsApp kan matakin gwamnatin jihar na rage lokacin zuwa aiki.

Nasir Dikko ya ce:

"Gwamna Namadi ya san daraja da mutuncin ma'aikata, yana daga cikin dalilin da ya sa mutane ke sonsa, yana kawo tsare-tsare da za su taimaka wa ma'aikata.
"A irin wannan lokaci na watan Ramadan, Musulmi na bukatar isasshen lokaci domin yin ibada, kamar ya san abinda ke zuciyarmu, ya rage lokacin zuwa ofis."

Dikko ya kuma jinjinawa gwamnan akan shirin ciyar da al'umma da ya shirya yi a watan azumi, yana mai cewa:

"Mallam, ana cikin mawuyacin hali, talaka na karbar kida, amma wannan shirin ciyarwar zai rage radadin talauci ga mutane da yawa."

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan APC ya ware N2.8bn domin dafa abincin buda baki, ya kafa kwamiti

Dikko wanda ya yi wa gwamnan fatan alkairi ya kuma roki ma'aikatan jihar da su saka masa ta hanyar yin aiki tukuru da rike amanar aikin da suke yi.

Ramadan: Za a ciyar da mutane a Jigawa

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Jigawa tace za ta ciyar da mutane 171,900 a kowacce rana na tsawon kwanakin watan Ramadan.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Auwalu Sankara ya bayyana cewa gwamnati ta kafa wasu cibiyoyin rabon abincin guda biyu a kowacce gunduma ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel