Ma’aikata Za Su Rasa Ayyukansu, Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Amincewa da Rahoton Oronsaye

Ma’aikata Za Su Rasa Ayyukansu, Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Amincewa da Rahoton Oronsaye

  • Yayin da Shugaba Tinubu ya amince da amfani da rahoton Oronsaye, Sanata Shehu Sani ya yi martani kan lamarin
  • Sanatan ya ce tabbas wannan wani mataki ne mai kyau na ganin an rage yawan kashe kudaden sai dai a yi taka tsan-tsan
  • Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce wannan mataki na Tinubu zai jawo rasa ayyukan wasu ma’aikata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - A jiya Litinin ce 26 ga watan Faburairu, Shugaba Tinubu ya amince da rushe wasu hukumomi da kuma hade wasu wuri daya.

Shugaban ya dauki shawarar rahoton Stephen Oronsaye wanda aka aiwatar tun a shekarar 2011.

Kara karanta wannan

Babban labari: Tinubu ya shirya amfani da rahoton Oronsaye, zai yi wani babban sauyi a Najeriya

Shehu Sani ya yi magana kan amfani da rahoton Oronsaye
Sani ya fadi amfani da kuma matsalar amincewa da rahoton Oronsaye. Hoto: Sani Shehu, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Martanin Shehu Sani kan rahoton Oronsaye

Wannan mataki a cewar rahoton zai rage yawan kashe kudade babu dalili da gwamnatin ke yi madadin gina kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Sanata Shehu Sani ya yi martani kan wannan mataki inda ya ke ganin za a iya samun matsala dalilin haka.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce wannan mataki na Tinubu tabbas abu ne mai kyau amma za a iya samun matsala.

Sanatan ya ce a wani bangaren za a iya cewa mutane da dama za su iya rasa ayyukansu a kasar.

Shawarar da Shehu Sani ya bayar

Ya bukaci shugaban da tawagarsa da su yi taka tsan-tsan wurin neman rage yawan kashe kudaden yayin da ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su rasa aikinsu.

Ya ce:

“Rahoton Orusanya ya yi abin a yaba wurin rage yawan kashe kudade a kasar, wannan wani mataki ne na ci gaba a bangaren rage kashe kudade.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

“Sai dole za a yi taka tsan-tsan wurin neman rage yawan kashe kudaden saboda dubban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su iya rasa ayyukansu.”

Tinubu ya amince ta rahoton Oronsaye

A baya, kun ji cewa, Shugaba Tinubu ya amince da amfani da rahoton Stephen Oronsaye kan rage yawan kashe kudade.

Rahoton wanda aka yi shi tun a shekarar 2011 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Joanthan ya samu karbuwa yanzu.

Makasudin yin rahoton shi ne lalubo hanyar rage yawan kashe kudade wurin hadewa da kuma rusa wasu hukumomin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel