Ramadan: Gwamnan APC a Arewa Zai Biya Ma’aikata Rabin Albashi Domin Yin Azumi Cikin Walwala

Ramadan: Gwamnan APC a Arewa Zai Biya Ma’aikata Rabin Albashi Domin Yin Azumi Cikin Walwala

  • Yayin da aka shiga watan azumin wannan shekara, Gwamna Aliyu na jihar Sokoto ya yi albishir ga ma'aikatan jihar
  • Gwamnan ya ce zai fara biyan rabin albashin ma'ikatan jihar a daren yau Lahadi 10 ga watan Maris domin walwala a azumi
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani ma'aikacin jihar Sokoto kan wannan lamari domin tabbatarwa da kuma sanin ko ya samu goron azumin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya amince da biyan rabin albashi ga ma'aikatan jihar da 'yan fansho.

Gwamnan ya amince da biyan albashin ne kyauta ga dukkan ma'aikata tun daga malaman makarantun firamare da ma'aikatan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Sanatan PDP, Sodangi ya rasu a daren farkon watan Ramadan

Gwamnan APC zai sharewa ma'aikata hawaye yayin da ake cikin halin kunci
Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto zai gwangwaje ma'aikata da rabin albashi domin azumi cikin walwala. Hoto: Ahmad Aliyu.
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi hakan ne domin azumi

Wannan mataki na zuwa ne yayin da aka shiga daren watan azumin Ramdana a yau Lahadi 10 ga watan Maris, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Aliyu ya ce ya yi hakan ne domin tabbatar da cewa Musulmai a jihar sun gudanar da azumin wannan wata cikin walwala.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Abubakar Bawa ya fitar, cewar PM News.

Wace shawara ya ba 'yan kasuwa?

"Gwamnan zai taimaka wa ma'aikata domin yin azumi cikin walwala wanda za a fara a gobe Litinin."
"Gwamna Aliyu ya roki Musulmai a jihar da su yi amfani da wannan wata domin rokon ubangiji kan matsalolin da kasar ke ciki."
"Ya kuma bukaci 'yan kasuwa da masu hali wurin taimakawa wadanda basu da karfi domin samun rahama a wannan wata."

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

- Gwamna Aliyu

Legit Hausa ta ji ta bakin wani ma'aikaci a jihar Sokoto kan wannan abin alkairi da gwamnan ya yi.

Surajo Sa'adu Umar da ke ma'aikatar ilimi mai zurfi ya ce tabbas ya samu rabin albashinsa jim kadan bayan sanar da fara biyan kudaden a jihar

Ya godewa gwamnan inda ya ce tabbas ma'aikata su na jin jiki inda ya yi godiya kan taimakon da ya yi a kan lokaci.

"Gaskiya mun ji farin ciki sosai duba da yanayin da ma'aikata suka tsinci kansu a jihar Sokoto, gaskiya gwamna ya yi abin da ya dace.
"Idan da bai yi ba haka ba mutane za su sha wahala ganin yadda farashin abubuwa suka tashi, muna godewa Gwamna Dakta Ahmad Aliyu Sokoto."

Gwamna Idris zai raba hatsi tirela 200

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamna Nasir Idris ya amince da raba tirelolin hatsi har guda 200 kyauta ga al'umma.

Kara karanta wannan

Yadda gwamna a Najeriya ya ci mutuncin ciyaman din karamar hukuma a bainar jama'a, an yada bidiyon

Gwamnan ya ce ya yi haka ne domin tausayawa al'ummar jihar da suke cikin matsin halin rayuwa.

Gwamnan har ila yau, ya kuma yi alkawarin ci gaba da kawo tsare-tsaren da za su rage wa jama'a radadi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel