Gwamnantin jihar Jigawa ta gwangwaje ma’aikata da karin albashi, an samu karin bayani

Gwamnantin jihar Jigawa ta gwangwaje ma’aikata da karin albashi, an samu karin bayani

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta gwangwaje ma'aikatan jihar da karin albashin naira dubu 30 wanda za a ba da na tsawon watanni uku
  • Gwamnan jihar, Umar Namadi ne ya ba da umarnin fitar da kudin da nufin saukakawa ma'aikatan jihar radadin janye tallafin fetur
  • Haka kuma, gwamnatin jihar na shirin kaddamar da rabon kayan abinci, tallafin taki da kayan aikin noma ga ma'aikatan jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya amince da biyan ma'aikatan gwamnatin jihar karin albashin naira dubu 30 har na tsawon watanni uku.

Manufar karin albashin ita ce a rage wa ma'aikatan radadin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki matakai na saukakawa rayuwar ma'aikatan jihar
Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki matakai na saukakawa rayuwar ma'aikatan jihar bayan janye tallafin fetur. Hoto: @uanamadi
Asali: Twitter

Manufar ba da tallafin albashin na watanni uku

Kyautar albashin na daga cikin yarjejeniyar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar da gwamnatin jihar suka cimmawa, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban ma’aikatan jihar Muhammad Dagaceri mai dauke da sa hannun kakakin ma'aikatar Ismail Ibrahim.

Mista Dagaceri ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta bayan cire tallafin man fetur.

Gwamnati ta shirya gwangwaje ma'aikatan jihar

Dagaceri ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta fara rabon kayan abinci ga ma’aikatan, inda ya jaddada cewa tuni aka kafa kwamitin da zai tabbatar da gudanar da aikin cikin sauki.

Daily Trust ta ruwaito sanarwar na cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta samar da matakan saukaka matsalolin sufuri da ma'aikatan gwamnati ke fuskanta a jihar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Zulum ta yi wa ma'aikata sha tara na arziki, an samu ƙarin bayani

“A kan shirin 'tallafawa noma daga ma'aikatan Jigawa (JWASS)', nan ba da jimawa ba za a samar da taki da sauran kayan amfanin gona ga ma’aikatan kamar yadda Gwamna Umar Namadi ya umarta.”

- In ji sanarwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel