Kungiyar NLC Ta Bukaci N794,000 Ga Ma'aikata a Yankin Tinubu, Bayanai Sun Fito

Kungiyar NLC Ta Bukaci N794,000 Ga Ma'aikata a Yankin Tinubu, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake cikin matsin tattalin arziki, kungiyar NLC ta bukaci N794, 000 a matsayin mafi karancin albashi
  • Kungiyar ta bukaci hakan ne ga ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma inda Shugaba Bola Tinubu ya fito
  • Shugabar kungiyar a yankin, Funmi Sessi, ita ya bayyana haka a yau Alhamis 7 ga watan Maris a Legas a wani taro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Kungiyar Kwadago ta NLC ta bukaci mafi karancin albashi N794, 000 ga ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma.

Vanguard ta rahoto cewa shugabar kungiyar a yankin, Funmi Sessi ita ya bayyana haka a yau Alhamis 7 ga watan Maris a Legas.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta mika sabuwar bukata ga gwamnati game da mafi karancin albashi

NLC ta bukaci dubu 794 a matsayin mafi karancin albashi
Kungiyar ta bayyana haka ne a Legas da ke yankin Kudu maso Yamma. Hoto: Bola Tinubu, Joe Ajaero.
Asali: Twitter

Albashi: Menene NLC ke cewa a yankin Tinubu?

Funmi ta ce wannan bukata ta biyo bayan amincewa da dukkan mambobin kungiyar suka yi a yankin, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sessi ya fadi hakan ne yayin taron tattaunawa kan mafi karancin albashin a wanda ministan kudade, Wake Edun ke jagoranta.

Funmi ta ce kiran karin mafi karancin albashin ya zama dole ganin yadda komai ya yi tsada a Najeriya, cewar rahoton.

Ta ce abin takaici ne kuma ba za su amince da yadda wasu gwamnoni basu iya biyan mafi karancin albashin a yanzu ba.

Tinubu ya kafa kwamitin mafi karancin albashi

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai, TheCable ta tattaro.

Shugaba Tinubu ya fito ne daga yankin Kudu maso Yamma inda kungiyar ke neman karin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

A ranar 30 ga watan Janairun 2024 ne Tinubu ya kafa kwamitin duba mafi karancin albashin mai dauke da mambobi 37.

NLC ta bukaci N500,000 mafi karancin albashi

Mun ruwaito muku cewa kungiyar kwadago ta NLC za ta nemi naira dubu 500 a matsayin mafi karancin albashi a kasar.

Wannan bukata tata na zuwa ne yayin da za a fara sauraron ra'ayoyin jama'a kan sabon tsarin mafi karancin albashin.

A yau Alhamis ce 7 ga watan Maris za a fara taron jin ra'ayin jama'a na shiyya-shiyya kan sabon tsarin albashi a Legas, Kano, Enugu, Akwa Ibom, Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel