Albashinmu Bai da Yawan da Ake Tunani, Yayi Kadan Inji Mataimakin Shugaban Majalisa

Albashinmu Bai da Yawan da Ake Tunani, Yayi Kadan Inji Mataimakin Shugaban Majalisa

  • Wasu sun kawo shawarar a rage albashin da ake biyan ‘yan majalisar tarayya domin ganin an rage kashe kudi a gwamnati
  • ‘Yan majalisar wakilai sun maida raddi cewa kudin da suke karba ba su isa a yi aikin da ake so saboda hauhawar farashi a yau
  • Benjamin Kalu yana ganin zaftare bangaren albashin ‘yan majalisa ba zai magance matsalar tattalina arzikin Najeriya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Benjamin Kalu ya koka a game da albashin da ake biyan ‘yan majalisar tarayya, ya ce kudin bai isa suyi aikinsu da kyau.

Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyan ya bayyana wannan a ranar Litinin da tashar talabijin Channels tayi hira da shi.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

Majalisa
'Yan majalisar tarayya Hoto: House of Representatives/Getty Images
Asali: Facebook

Ashe albashin 'yan majalisa yayi kadan?

Benjamin Kalu ya ce a tsarin albashin da suke kai a yau, kudin da ake biyansu ba zai isa suyi ayyukan da aka zabe su domin su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar ya fadi wannan a matsayin martani a daidai lokacin da ake neman ‘yan majalisa su rage kudin da suke ci.

Hon. Ben Kalu yake cewa zaftare rabin albashin majalisar tarayya ba zai zama mafita ba a halin matsin tattalin arzikin da aka shiga.

Maganar Ben Kalu a kan albashin Majalisa

"A yanzu, idan muna maganar albashin majalisar tarayya. Na fadi wannan sau da dama, bai da yawa kamar yadda mutane ke tunani."
"Albashi dabam da alawus, wanda aka tanada domin ayyukan da mazabunmu suka tura mu."
"Babu wanda aka yarda ya taba alawus. Albashi ne na mu. Duk alawus da aikinsa, idan ka kashe ta inda bai dace ba, za a hukunta ka."

Kara karanta wannan

"A shigo da abinci" TUC ta gano hanya 1 da zata share hawayen talakawa, ta aike da saƙo ga Tinubu

- Hon. Ben Kalu

Punch ta rahoto Hon. Kalu yana cewa ko sun hakura da 50% ko 80% na albashinsu, ba zai yi tasirin kirki a kan tattalin arzikin kasar ba.

Hauhawar farashi ya cinye albashin majalisa

"Ina mai tabbatar maka cewa a halin da ake ciki a yau, hauhawar farashi da sauransu, abin da ake biyan ‘yan majalisar tarayya bai isa su je gida suyi aikinsu a mazabunsu."

- Hon. Ben Kalu

‘Dan majalisar na Abia ya ce kudin mota da na rike ofis sun tashi saboda hauhawar farashi yayin da wasu suke kokawa da albashin na su.

Ana da labari bayanai sun fito bayan zaman da jami’an gwamnatin tarayya suka yi da wakilan kwadago domin hana a cigaba da zanga-zanga.

Shugaban NLC ya ce ba za su fasa abin da aka shirya ba, kuma dole gwamnati ta bada kariya a yi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel