NLC da TUC Sun Ci Karo Kan Mafi Ƙarancin Albashi a Abuja, Wasu Jihohi 6 Sun Gabatar da Buƙatarsu

NLC da TUC Sun Ci Karo Kan Mafi Ƙarancin Albashi a Abuja, Wasu Jihohi 6 Sun Gabatar da Buƙatarsu

  • Manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun samu sabanin adadin da ya kamata ya zama mafi ƙarancin albashi a Abuja
  • Kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa domin nazari kan albashin ma'aikata ya fara sauraron ra'ayoyin jama'a kan sabon mafi ƙarancin albashi
  • NLC da TUC sun gabatar da bukatarsu kan sabon albashin a jihohi da dama, sun buƙaci a hukunta duk gwamnan da ya ƙi aiwatarwa a jiharsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta gabatar da N709,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta gabatar da wannan adadin kudi ne a wurin taron jin ra'ayoyin jama'a kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: 'Yan majalisa sun ba Tinubu shawara kan albashin da ya kamata a biya ma'aikata

NLC da TUC sun bada alkaluman da suka saɓa wa juna a Abuja.
Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ci Karo da Juna Kan Mafi Karancin Albashi Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

TUC ta saɓawa NLC a Abuja

A daya bangaren kuma kungiyar ‘yan ƙwadago (TUC) ta bada shawarar N447,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin kwadagon biyu sun ce sun yanke wannan adadin kuɗi da suka saɓa wa juna a matsayin mafi ƙarancin albashi bisa la'akari da halin da ake ciki a yanzu.

Yadda ƴan kwadago suka faɗi buƙatarsu a jihohi

Sai dai jihohin Kwara, Nasarawa, da Neja sun gaza gabatar da wani adadin kudi da suke gani shi ya fi dacewa da albashin ma'aikatansu.

An tattaro cewa jihar Filato ce kawai ta gabatar da N81,000 domin tantancewa adadin a matsayin sabon mafi karancin albashi na kasa.

Amma a jihar Akwa Ibom, ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun bukaci N850,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Sunny James ya jaddada cewa duk gwamnan da ya ki biyan N850,000 to a daure shi a gidan yari.

James a lokacin da yake gabatar da takardar bukatarsu ya ce: "Duk gwamnan jihar da ya ki biyan sabon mafi karancin albashi to a daure shi."

Rahoton Vanguard ya nuna cewa ƴan kwadago a shiyyar Kudu maso Yamma sun nemi N794,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Shugabar NLC reshen jihar Legas, Misis Funmi Sessi, ce ta bayar da wannan shawarar ga gwamnati mai mulki a ranar Alhamis.

Wane adadi NLC ta ƙasa za ta nema?

Wasu rahotanni na nuna cewa kungiyar kwadago za ta nemi N500,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.

A yayin da za a fara taron jin ra'ayin jama'a na shiyya-shiyya kan sabon tsarin albashi a yau (Alhamis), kungiyar za ta yanke matsayarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel