Masu Garkuwa Da Mutane
Jami'an rundunar yan sanda a jihar Kogi sun yi nasarar ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su daga wani Otel da ke yankin Eleite a hanyar titin Lokoja-Ajaokuta.
Zababben ‘dan majalisar Gbako ya sha da kyar ne a sakamakon harin da aka kai masa a Gyado a Benuwai. A makon da ya gabata aka yi zaben jihohi, Dajoh ya ci zabe.
‘Yan Bindiga sun kashe wani Shugaban yakin neman zaben APC da suka yi garkuwa da shi. Ana tunanin Chisom Lennard ya rasu ne yana hana ‘yan daba yin magudi.
Za a ji labari 'Yan sandan reshen jihar Legas sun yi ram da wani mutum mai shekara 36 da zargi mai ban al'ajabi. Nan da kimanin makonni biyu za a koma kotun.
Yan bindiga a Kaduna sun kai hari garuruwan Karimbu-Kahugu a karamar hukumar Lere a Kaduna a safiyar ranar Juma'a inda suka kashe dan fasto tare da sace matarsa
Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar kama wani matashi mai suna Thomas Ya'u dan shekara 20 kan zargin garkuwa da mahaifiyarsa ya karbi fansar N30m.
Ƴan sanda a jihar Zamfara sun yi babban kamu, sun cafke matar dake safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar. Matar ta daɗe tana gudanar da wannan baƙar sana'ar.
Jami'an rundunar sojin Najeriya sun kai samamen kwantan bauta kan mafakar masu garkuwa da mutane a Kuros Riba, sun ceto kwamishinar harkokin mata da aka sace.
Mista Johnson Ademola Adesola ya rasu yana kokarin cire kudi a layin bankin Wema. Jami’ar jihar Legas ta tabbatar da rasuwar Adesola da yadda abin ya faru.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari