‘Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Jihar Zamfara, Sun Sace Mutum Fiye Da 100

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Jihar Zamfara, Sun Sace Mutum Fiye Da 100

  • ‘Yan bindiga sun kai kazamin hari kan al’umman garuruwan jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutum sama da 100
  • Masu tayar da kayar baya sun kai hari garuruwan Kanwa, Kwabre, Yan Kaba da Gidan Goga a kananan hukumomin Maradun da Zurmi
  • Yawancin wadanda harin na ranar Lahadi ya cika da su kananan yara masu shekaru 14-16 da kuma mata ne

Zamfara - Rahotanni sun kawo cewa tsaregun ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu garuruwan Zamfara inda suka yi garkuwa da mutum fiye da 100 da suka hada da mata da yara.

An tattaro cewa maharan sun kai hari garuruwa da dama ciki harda kauyen Kanwa a karamar hukumar Zurmi ta jihar a ranar Lahadi, Sahara Reporters ta rahoto.

Jihar Zamfara
‘Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Jihar Zamfara, Sun Sace Mutum Fiye Da 100 Hoto: Vanguard
Asali: UGC

'Yan ta'adda sun farmaki al'ummar garuruwan Kanwa, Kwabre, Yan Kaba da Gidan Goga

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Kwamishinan labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, da mazauna garuruwan sun tabbatar a ranar Litinin cewar an sace mutum fiye da 40 a kauyen Kanwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, wani mazaunin garin Kwabre a karamar hukumar ta Zurmi ya bayyana cewa an sace akalla mutum 37 wadanda yawancinsu mata da yara ne.

Wani mazaunin kauyen Kanwa ya ce:

“Yanzu haka, kauyen Kanwa ya zama kamar kufai, ‘yan bindigar sun raba kansu gida biyu sannan suka farmaki garin. Sun yi awon gaba da yara tsakanin shekaru 14 zuwa 16 da kuma mata.”

An kuma tattaro cewa a garuruwan Yankaba da Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun, an sace akalla mutum 38 yayin da suke hanyarsu ta zuwa aiki a gonakinsu.

Da yake korafi kan lamarin, VOA ta rahoto cewa kwamishinan labaran ya yi ikirarin cewa yan ta’addan na amfani da wadanda suka sace a matsayin kariya daga hare-haren rundunar sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wasu Mutane Na Hada Miliyan N20 Zasu Kaiwa Bello Turji Saboda Ya Barsu Su Sarara

Mutanen Garin Goga na neman sulhu da Turji

A gefe guda, mun kawo a baya cewa al'ummar Gidan Goga sun fara wani yunkuri na samawa kansu salama daga yawan hare-haren ta'addanci da yan bindiga ke kai masu.

Yanzu mutanen garin sun fara tara kudi naira miliyan 20 domin baiwa kasurgumin shugaban yan ta'adda da ya addabi jihohin Zamfara, Sokoto da Neja, Bello Turji a kokarinsu na ganin ya sakar masu mara suyi fitsari.

Sun aikata hakan ne domin yin sulhun zaman lafiya da Turji tare nemawa kansu kariya daga hare-harensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel