Fasinjoji Sun Jigata Yayin da Masu Garkuwa da Mutane Suka Hari Bas Kan Titin Legas zuwa Ibadan

Fasinjoji Sun Jigata Yayin da Masu Garkuwa da Mutane Suka Hari Bas Kan Titin Legas zuwa Ibadan

  • Miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai mummunan hari kan motar bas mai mazaunin mutum 18 a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan
  • ’Yan ta’addan sun bayyana ne daga daji inda suka budewa motar wuta yayin da fasinjoji suka kwanta a cikin motar don gujewa harsasai
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ya tabbatar da cewa jami’ai sun bi kan ‘yan ta’addan inda suka bude musu ruwan wuta har suka arce zuwa daji

Legas - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki kan fasinjoji dake kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Legas zuwa Ibadan
Fasinjoji Sun Jigata Yayin da Masu Garkuwa da Mutane Suka Hari Bas Kan Titin Legas zuwa Ibadan. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

‘Yan Bindigan sun kaddamar da farmakin ne a ranar Talata kuma sun kai harin ne yayin da suke sanye da kayan sojoji.

‘Yan bindigan sun bayyana daga daji inda suka fara harbin fasinjoji dake cikin bas mai mazaunin mutum 18 a hanyar Sagamu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Fasinjojin da lamarin ya shafa sun kwanta a cikin motar domin gujewa harsashin ‘yan bindigan, jaridar TheCable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da aka dauka na yadda lamarin ya faru, wasu daga cikin fasinjojin da lamarin ya shafa sun bayyana yadda direbansu ya kasa sarrafa motar yayin da ake harbin.

Bidiyon ya bayyana wasu daga cikin fasinjojin da suka samu raunika.

‘Yan Sanda sun magantu

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, a yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, a ranar Laraba yace ‘yan bindigan masu garkuwa da mutane ne da suka je aiwatar da mugun nufinsu a kan babbar hanyar.

Oyeyemi yace jami’an ‘yan sandan dake kan babbar hanyar sun yi artabu da ‘yan bindigan.

“Wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka tsere daga wurin sun arce da miyagun raunika. A lokacin, jami’anmu sun fada daji domin samo gawawwakin wasu daga cikin ‘yan bindigan.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Kan Mutane a Shingen 'Yan Sanda, Rayuka Sun Salwanta

- Yace.

Farmakin ‘yan bindiga na cigaba da yawaita

A cikin watanni kadan da suka gabata, ana ta samun karuwar rahotanni kan yawaitar fashi da makami da garkuwa da mutane a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

A ranar 28 ga watan Oktoba, an sace masu ababen hawa da har yanzu ba a san yawansu ba a kan titin Legas zuwa Ibadan inda suka hada da Agbaje, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ibadan.

Agbaje ya samu ‘yanci bayan kwashe kwanaki biyu a hannun masu garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng