An yi irin na Hanifa: An Kama Matashi Ya Yi Garkuwa da ‘Dan Shekara 5, Ya Kashe Shi

An yi irin na Hanifa: An Kama Matashi Ya Yi Garkuwa da ‘Dan Shekara 5, Ya Kashe Shi

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta damke matashin da ake zargin ya kashe wani 'dan karamin yaro
  • Anas Auwal zai amsa laifin garkuwa da wani Abba Yahuza mai shekara 5, daga nan kuma ya hallaka shi
  • Da farko Auwal ya nemi a biya N5m, amma da abin ya gagara sai ya kashe yaron, ya birne shi a cikin rami

Bauchi - Wani matashi mai shekara 25 a Duniya ya shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin hallaka wani ‘dan yaro mai shekara 5 da haihuwa.

A yau ne jaridar Punch ta rahoto cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama Anas Auwal, ana tuhumarsa da kisan yaron da ya dauke.

Anas Auwal mazaunin kauyen Tsangaya ne a karamar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi. Ana tuhumarsa da yin garkuwa da Abba Yahuza.

Rahoton yace bayan Auwal ya sace wannan yaro zuwa dakinsa a kauyen Tsangaya, ya tuntubi iyayensa su biya fansar Naira miliyan biyar.

Babu N5m - Iyayen Abba Yahuza

Mahaifin wannan karamin yaro ya fadawa matashin bai da wadannan miliyoyin kudi da zai bada domin ya iya fansar Abba daga hannunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashin ya yaudari marigayin da mika masa alewa, daga nan ya rufe shi a dakinsa.

Bauchi CP
Tsohon Kwamishinan 'Yan Sandan Bauchi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A ranar Alhamis dinnan, Kakakin rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya shaidawa manema labarai yadda aka yi.

Asiri zai tonu!

SP Wakil ya fadawa ‘yan jarida cewa wanda ake tuhuma ya shake yaron ne har ya tafi barzahu bayan ya fahimci cewa ya riga ya gane fuskarsa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, CP Umar Mamman Sanda ya bada umarnin a gurfanar da wanda ake tuhuma a kotu domin ayi shari’a.

Bincike ya nuna da ranar 11 ga watan Oktoban 2022 ne Anas Auwal ya yi amfani da alewa, ya sace Abba Yahuza, ya kuma boye shi a cikin dakinsa.

Da aka gagara biyan N5, 000,000.00, kuma saurayin ya ji tsoron an gane shi, sai ya kashe yaron cikin dare, ya saka shi a buhu, ya birne shi a rami.

Haka aka yi da Hanifa

Kwanakin baya haka aka ji labarin wani Abdulmalik Tanko da ya sace Hanifa Abubakar. Daga baya wannan mutumi ya karyata zargin kisan.

Amma matar wanda ake zargin, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a kotu, ta fallasa yadda mai gidanta ya yi mata karya, ya kawo mata 'yar yarinyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel