Jarumin ‘Dan Banga Ya Harbe ‘Yan Bindiga da Suka Bude Wuta a Kasuwa a Zamfara

Jarumin ‘Dan Banga Ya Harbe ‘Yan Bindiga da Suka Bude Wuta a Kasuwa a Zamfara

  • Wasu miyagun ‘yan bindiga sun aukawa kasuwar Gidan Goga a Zamfara, sun shiga budawa jama’a wuta
  • ‘Yan banga sun yi kokarin maida martani, har aka samu wani jarumi da ya kashe wasu ‘yan bindiga biyu
  • Amma daga baya abin ya fi karfin ‘yan banga, miyagun sun yi sata a kasuwar, suka kona dukiyoyin jama'a

Zamfara - A ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba 2022, ‘dan sa-kai na kato-da-gora yayi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Daily Trust ta rahoto cewa wani ‘dan kato-da-gora ya nemi ya hana ‘yan bindiga kai hari a kasuwar Gidan Goga a karamar hukumar Muradun.

Gungun ‘yan bindiga sun shiga kasuwar nan da ke kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi, suka rika harbin Bayin Allah babu gaira-babu dalili.

Wasu mutane uku da suka nemi su tsere, sun gamu da ajalinsu nan-take a hannun ‘yan bindigan. A ciki akwai wani mutumin Kauran Namoda.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

Da ya lura da abin da yake faruwa, wani ‘dan kato-da-gora da yake rike da bindiga a lokacin, sai ya shiga buda masu wuta, ya kuma yi sa’a a kansu.

Kasuwa a Zamfara
Wata kasuwa a Zamfara Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda abin ya kasance

“A lokacin da ‘yan ta’addan suka iso, sai suka rika buda wuta ga ‘yan kasuwa, daga nan aka shiga fagamniya, kowa yana neman mafita a kasuwar.”
“Amma akwai wani ‘dan banga rike da bindiga, sai ya yi ta harbin ‘yan bindigan, ya kashe biyu daga cikinsu nan-take. Daga nan sai ya canza wuri.
A nan ya cigaba da harbin miyagun a sa'ilin da abokan aikinsa sun sare.

- Shaida

Abin ya fi karfin 'yan banga

Majiyar ta shaidawa jaridar cewa duk da kokarin da wannan mutumi ya yi, ‘yan bindigan sun ci karfin jama’a a kasuwar, suka tafka irin ta’adinsu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyayensu, Ya Dauko Marayu, Zai Kashe Masu N300m

“’Yan bindigan sun nemi a karo masu mutane, sai suka fi karfin ‘yan bangan. Suka mamaye kasuwar da kowa ya tsere, suka saci kaya, suka kona babura.
Sun kona shaguna, sannan suka yi tafiyarsu. Bayan ‘yan bindigan sun tafi, an samu kayan sojoji."

- Shaida

‘Yan jarida sun nemi jin ta bakin ‘yan sanda, amma ba a iya tuntubar kakakin rundunar na reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu a jiya ba.

Zulum zai taimaki marayu

An rahoto cewa Gwamnatin jihar Borno ta ware N300m domin marayu su samu damar da za su je makarantun boko, saboda sun rasa iyayensu a yaki.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bukaci a taimakawa yaran ‘yan sa-kai da suka mutu a yakin Boko Haram, wanda yanzu haka ba su da masu kula da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel