Bene Ya Ruguzo a Kano, an Samu Asarar Rai da Raunata Wasu Mutane

Bene Ya Ruguzo a Kano, an Samu Asarar Rai da Raunata Wasu Mutane

  • Mutum ɗaya ya rasu bayan wani bene mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Mutane uku sun samu raunuka kuma an ceto su daga ƙarƙashin baraguzan ginin wanda ya rushe lokacin da ake aiki a cikinsa
  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin acikin wata sanarwa a ranar Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu uku suka jikkata bayan wani bene mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe a jihar Kano.

Benen ya rushe a kan titin Sultan da ke cikin birnin Kano a safiyar ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin shekarar 2026.

Bene ya ruguzo a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'in hulɗa da jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bangar siyasa suka hallaka wani fitaccen malamin Islamiyya a Bauchi

Bene ya ruguzo a Kano

Saminu Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe yayin da ma'aikata ke aikin ginin.

"Sakamakon rushewar ginin, mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban."

- Saminu Abdullahi

Ya bayyana cewa an fara ceto mutum uku daga ƙarƙashin baraguzan ginin, yayin da jami'an ceto suka ci gaba da ƙoƙarin kai wa wurin mutum na huɗu da ya maƙale a ƙarƙashin ginin.

Sai dai daga bisani an gano cewa mutumin ya rasu, rahoton da jaridar TheCable ta kawo ya tabbatar da hakan.

Yadda lamarin ya faru

Wasu shaidu sun ce ma'aikatan sun lura da alamun cewa ginin na dab da rushewa yayin da suke aiki a saman bene, lamarin da ya sa suka yi gaggawar tserewa domin tsira da rayukansu.

Wani shaidar gani da ido da ya bayyana sunansa da Yaro kawai ya bayyana cewa:

"Injiniyan ya lura da alamun cewa ginin zai rushe, nan take ma'aikatan suka ruga domin tsira da rayukansu."

Kara karanta wannan

Lauya ya dauko da zafi, ya maka Tinubu da Ministan ayyuka kara gaban kotu

"An ceto mutum uku, ciki har da mai gadin wurin da kuma ɗaya daga cikin abokaina. An kai su asibitin kwararru na Sir Muhammadu Sanusi domin samun kulawa bayan sun samu raunuka."
Gini ya rufto a jihar Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan rugujewar gini

Mimbari ya ruguzo da Gwamna Adeleke

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu rugujewar wani mimbarin siyasa da mutane, ciki har da Gwamna Ademola Adeleke, suke kai a jihar Osun da ke yankin Kudu maso Yamma.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wani gangamin siyasa da aka gudanar a Ijebu-Jesa yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamna a Osun.

Wani bidiyo na dakika 30 ya nuna lokacin da mimbarin ya kife alhali Gwamna Adeleke da mataimakinsa, Kola Adewusi na kan shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com