Zargin Ta’addaci: Gwamnati ta Nemi Jami’an tsaro Suyi Ram da ‘Yar Takarar PDP

Zargin Ta’addaci: Gwamnati ta Nemi Jami’an tsaro Suyi Ram da ‘Yar Takarar PDP

  • Gwamnatin jihar Kogi ta zargi Natasha Akpoti Uduaghan da alaka da wanda ake tuhuma da ta’addanci
  • Kwamishinan yada labaran jihar ya fitar da jawabi, yana neman jami’an tsaro su kama Natasha Uduaghan
  • Kingsley Fanwo yace ‘yar siyasar tana da alaka da wani wanda ake zargin shi da kashe masu ibada a coci

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi tayi kira ga shugabannin jami’an tsaro su gayyaci Natasha Akpoti Uduaghan bisa zargin ta da hannu a ta’addanci.

Rahoton PM News yace Kwamishinan yada labarai a jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fitar da jawabi yana kira a binciki Natasha Akpoti Uduaghan.

Kingsley Fanwo ya zargi Natasha Akpoti Uduaghan da cewa tana da alaka da wani Safiu, wanda ake zargin shi ya kai hari a cocin katolika da ke Owo.

Natasha Uduaghan wanda Lauya ce kuma ‘yar siyasa, ta na takarar Sanata ne a 2023 a jam’iyyar PDP. Za a samu wannan rahoto a jaridar This Day.

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

Gwamnatin Kogi tace wannan Safiu yana cikin wadanda ake zargi da kai hari a gidan hali na Kuje da kuma ga rundunar jami’an tsaro a Najeriya.

A jawabin da ya fitar, Fanwo yace ‘yar siyasar ta nuna barazana ce ita ga al’umma saboda alakanta kan ta da tayi da wanda ake zargin ‘dan ta’adda ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Natasha Akpoti
Natasha Akpoti Uduaghan da Mai gidanta Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

“Abin damuwa ne ga PDP da Natasha za ta fito tana alakanta kanta da Safiu, wanda ake zargi da laifin kai mugun hari a cocin Owo da ya kashe masu ibada.
Shi ne kuma ake zargi da kai hari a gidan gyaran hali na Kuje da rundunar jami’an tsaro a gida da wajen jihar Kogi.
Ganin yadda jami’an tsaro suka cafke babban wanda ya addabi jama’a, abin kwantar da hankali ne. Ta’adi bai da jam’iyya, a hukumta mara gaskiya, ko wanene.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Yi Ram da Gagararren Dilallin Kwayoyi

Kafin 2016, yankin tsakiyar Kogi ya kasance mafakar ‘yan ta’adda, akwai gungunan kungiyoyin ta’addanci, ana kai wa daruruwan mutane hari da rana-tsaka.
Gwamnati ba za ta bari a komawa abin da ake yi a da ba.

- Kingsley Fanwo

Kwamishinan labaran yace jam’iyyar PDP ta amsa cewa Safiu yana cikin ‘ya ‘yanta, hakan na nufin su na da hannu a 52% na ta’adin da ake yi a Kogi.

Yarjejeniya da Turkiyya

An samu rahoto Muhammadu Buhari da Recep Tayyip Erdoğan sun shiga yarjejeniya kan harkar tsaro a madadin kasashen Najeriya da Turkiyya a 2021

Jakadan kasar Turkiyya yace makaman da ake sauraro a sanadiyyar yarjejeniyar su na hanya, kayan aikin za su zo a daidai lokacin da ake kukan tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel