Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Abin da Ya Jawo Aka Fara Samun Saukin Matsalar Tsaro

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Abin da Ya Jawo Aka Fara Samun Saukin Matsalar Tsaro

  • Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ya yi jawabi a wajen taron da DIA ta shirya a shekarar bana
  • Hadimin shugaban kasar yace ana samun zaman lafiya a dalilin dabarun da jami’an tsaro suka fito da su
  • Tun a 2015, Janar Babagana Monguno shi ne Mai ba Shugaban Najeriya shawara game da sha’anin tsaro

Abuja - Babagana Monguno ya bayyana cewa sababbin dabarun da jami’an tsaro suka fito da shi, su na kawo nasarori wajen yakar matsalar tsaro.

Daily Trust ta rahoto Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya yana mai wannan jawabi a wajen wani taro da hukumar DIA ta shirya a garin Abuja.

Duk shekara DIA ta kan yi irin wannan taro, a bana an tattauna ne game da tasirin hadimai da masu bada shawara a wajen inganta tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

Hukumar tsaron ta kuma kaddamar da wasu gine-gine da wuraren aiki da nufin tattara bayanan da za su rika taimakawa jami’anta wajen sha’anin tsaro.

Tasirin sababbin dabaru

Babagana Monguno yace sojoji da sauran dakaru sun zo da sababbin salo wajen magance kalubalen da ake fuskanta a wasu yankunan kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba shugaban kasan shawara a kan sha’anin tsaro yace ana fama da barazanar ‘yan ta’adda da tsageru a Kudu maso gabas da Arewa maso gabas.

Manjo Janar Babagana Monguno
Babagana Monguno da Hafsun Sojoji Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto Monguno yana cewa barazanar da ake fuskanta a Najeriya sun hada da satar danyen mai, garkuwa da mutane, da satar dababbobi.

A cewarsa, yanzu an cin ma nasara a wasu yankunan musamman a wajen yakar masu fasa bututun mai da kuma wadanda ke fafutukar a raba Najeriya.

Duk da zaman lafiyan da aka samu a baya-bayan nan, Hadimin yace akwai bukatar a karfafawa irin kokarin da rundunar sojoji suke yi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Tabbatar da tsaro: An kama wasu masu hakar ma'adinai ba bisa kai'da ba a Abuja

Ana shiryawa zaben 2023

Shugaban CDI, Manjo Janar Samuel Adebayo yace makasudin taron da ake yi shi ne a duba yadda ake tunkarar sha’anin tsaro a fadin kasashen Duniya.

Janar Samuel Adebayo yake cewa a taron na bana, an dauki darasi kuma an fito da salon kawo zaman lafiya, musamman ganin zaben 2023 ya gabato.

An kashe mutane a Kebbi

Kwanaki an ji labari wasu mahara kimanin su 70 suka dura kauyen Tunga Rafi a karamar hukumar Augie da ke Kebbi, suka yi ta’adi a cikin dare.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya nuna ba su san da labarin ba, amma an iya tabbatar da cewa an hallaka mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel