Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

  • Yan sanda a jihar Adamawa sun yi ram da wani Isreal Emmanuel saboda yin garkuwa da kansa don karbar N1m daga mahaifinsa
  • Isreal ya hada baki a wasu abokansa uku ne ya tafi gidan abokinsa ya shafe kwana shida yayin da ake suke cinikin kudin fansar
  • Sai dai daya daga cikin abokan da aka wakilta ya karbo kudin fansar ya ha'inci sauran ya ce N500,000 aka biya, kuma aka bashi N200,000 kasonsa

Adamawa - Yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 19 a Jihar Adamawa, Isreal Emmanuel saboda shirya garkuwa da kansa tare da karbar Naira miliyan 1 na fansa daga mahaifinsa.

An tattaro cewa a ranar Asabar ne Emmanuel da wasu abokansa uku suka shirya garkuwar karya suka yi magana da mahaifinsa don karbar fansa, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano

Wadanda ake zargi
Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karbi Fansar N1m Daga Mahaifinsa A Adamawa. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kama Emmanuel wanda ya amsa cewa shi ya shirya garkuwa da kansa tare da abokansa biyu, Fartaci Mustapha da Zakka Nuhu, dukkansu daga karamar hukumar Mubi ta Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sandan na kan neman mutum na uku da ake zargi mai suna Abdulhamid Mohammed.

Yadda matasan suka shirya garkuwar

Emmanuel, mazaunin Mararraba Mubi, ya hadu da Zakka Nuhu a yankin Welcome to Mubi na garin Mubi, ya tafi Muvir a karamar hukumar Mubi ta Arewa ya boye kansa a gidan Fartaci Mustapha na kwana shida yayin da suke tattauna batun kudin fansar daga mahaifinsa.

Fartaci Mustapha ya kira mahaifin Isreal a waya, ya fada masa game da 'sace' dansa.

Bayan Fartaci ya gabatar da kansa ga Emmanuel a matsayin daya daga cikin masu garkuwar, ya mika waya ga Isreal kuma suka yi magana.

Kara karanta wannan

Zargin Safarar Sassan Bil Adama: An Bukaci Birtaniya Ta Saki Ekweremadu Da Matarsa

Isreal ya fada wa mahaifinsa cewa an sace ni kuma ana bukatar biyan kudin fansa kafin a sako shi.

Bayan kwana shida a Muvir, Isreal ya dawo gida Mubi ya hadu da sauran abokansa da suka hada baki suka matsa wa mahaifinsa har sai da ya biya Naira miliyan 1.

Ya umurci Fartaci da Abdulhamid su tafi daji a Mararaba Mubi don karbar fansar.

Mutane biyun sun hadu da Emmanuel amma Abdulhamid ne ya karbi kudin a inda aka ajiye musu.

Abdulrasheed ya ha'inci abokansa ya ce N500,000 kacal aka biya fansar

Abin takaici ga sauran wadanda suka shirya garkuwar, Abdulrasheed ya ce N500,000 kacal mahaifin Isreal ya biya matsayin fansa.

Isreal ya koma gida da N200,000 a matsayin kasonsa cikin N500,000 din, kuma tunda ya san ya yaudari abokansa sai ya tsere kafin, yan sanda su san da batun.

An kama sauran wadanda aka zargin bayan mahaifin Isreal ya kai korafi ofishin yan sanda, duk da cewa a lokacin bai san dansa ne ya yi garkuwa da kansa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Kakakin yan sandan Adamawa, SP Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatar da kamen ya bada tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa

Rundunar yan sandan Jihar Gombe a ranar Talata ta yi holen wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga iyalan wadanda suka sace.

A cewar kakakin rundunar, Mahid Abubakar, hakan na zuwa ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammad a Jihar Taraba, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel