Masu Garkuwa Da Mutane
Jami'an tsaro a jihar Bauchi sun yi nasarar sheke wani dan bindiga a karamar hukumar Toro ta jihar Nasarawa sannan suka yi nasarar ceto wasu mutum 3 da aka sace.
Masu garkuwa da mutane sun nemi naira miliyan 16 daga iyalan mata takwas da suka yi garkuwa da su a wani kauyen Abuja. Akwai matar sarkin garin cikin matan.
Wasu yan bindiga sun kai hari yankin Gandu na jami'ar tarayya ta Lafia a ranar Litinin, inda suka kashe wani makanike, sannan suka yi garkuwa da mata da diyarsa.
Yan bindiga sun kai hari kan al'ummar Dan-Honu da ke Millennium City, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka sace sabbin ma'aurata da malamin musulunci.
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi Ɗanmodi, ya nuna damuwarsa bisa yadda batun garkuwa da mutane ke yawaita a jihar, ya ce zai taimakawa jami'an tsaro.
Dakarun sojoji a jihar Taraba sun samu nasarar fatattakar wasu miyagun ƴan ta'adda masu yin garkuwa da mutane. Sojojin sun kuma ceto mutanen da suka sace.
A makon da ya gabata masu garkuwar suka sace basaraken a Abuja. Sai dai matar da suka sako, ta ce ba ta san inda za ta samo N100m don fansar mijinta da 'yayan ba
Ana fama da barayi da ‘Yan bindiga a Najeriya, a haka ne wasu Sojoji sun dauke ‘dan jaridan fadar Shugaban kasa, sun yi masa fashi a Abuja a makon da ya wuce.
Miyagun ‘yan bindiga su ka shiga Kujama, a nan su ka yi awon gaba da wani basarake, akwai ‘yan sandan da aka bindige da su ka yi kokarin dakile harin ‘yan bindiga.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari