Dubun Wasu Hatsabiban Yan Bindiga 8 da Suka Addabi Mutane Ya Cika a Jihar Kaduna

Dubun Wasu Hatsabiban Yan Bindiga 8 da Suka Addabi Mutane Ya Cika a Jihar Kaduna

  • Yan sanda sun kama yan bindiga takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a sassa daban-daban na jihar Kaduna
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya faɗi sunayen waɗanda aka kama
  • A cewarsa, ana zargin su ne suka yi garkuwa da sakataren tsare-tsaren jam'iyyar APC na Kaduna, Kawu Yakassai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon .shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.

Yan sanda sun kama tawagar masu garkuwa a Kaduna.
Dakarun yan sanda sun kama tawagar masu garkuwa 8 a jihar Kaduna Hoto: PoliceNG
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan, Mansir Hassan, ya ce jami'an tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne a maɓoyarsu da ke gonar Nuba.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yan ta'adda da dama sun mutu yayin da suka dasa bam ya tashi da su a jihar Borno

A wata sanarwa da kakakin yan sandan ya fitar ranar Alhamis, ya ce rahoton masaniyar farko ya nuna irin ta'addancin waɗanda aka kama, cewar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya bayyana cewa rahoton binciken farko da aka gudanar da ya nuna ƴan bindigan da aka kama suna da hannu a garkuwa da sakataren tsare-tsaren APC na Kaduna, Kawu Yakassai.

Sunayen ƴan bindigan da aka kama

Kakakin 'yan sandan ya ambaci sunayen ƴan bindigan da aka kama, sun haɗa da Bello Suleiman, Ismail Abubakar, Usman Suleiman, Umar Suleiman, da Isah Lawal, duk daga ƙauyen Farin Kasa, karamar hukumar Soba.

Sauran sun kunshi Abubakar Bello, Ibrahim Mu’azu da kuma Umar Suleiman duk a jihar Kaduna, in ji Mansir Hassan.

Ya kuma bayyana cewa shugaban tawagar ƴan bindiga mai suna, Hanazuwa, ya gudu amma jami'an tsaro na ci gaba da bin diddiginsa.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

A cewarsa, hukumar yan sanda zata gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kuliya bayan kammala bincike, rahoton Leadership.

CP ya yabawa jami'an tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Musa Garba, ya yabawa jami’an da suka kama wadanda ake zargi da hannu a garkuwa da mutane.

Ya kuma roƙi dakarun su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a bukukuwan kirsimeti da ke tafe.

Yan Bindiga Sama da 50 Sun Bakunci Lahira a Taraba

A wani rahoton na daban Yan sanda tare da sojoji, yan banga da mafarauta sun halaka yan bindiga sama da 50 a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya ce sun samu wannan nasara ne ranar Talata da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel