Jami'an Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Arewa

Jami'an Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Arewa

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wasu gunguj ƴan ta'adda masu garkuwa mutane
  • Jami'an ƴan sandan sun samu nasarar cafke miyagun ne a wani sumame da suka kai a maɓoyar ƴan ta'addan
  • Bincike dai ya nuna ƴan ta'addan su ne suka yi garkuwa da sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu mutane bisa zarginsu da hannu wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami a sassan jihar.

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce jami’an tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne a maɓoyar su da ke gonar Nuba, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun cafke babban shugaban yan ta'addan ISWAP, bayanai sun fito

Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane
Jami'an yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna da alhakin yin garkuwa da sakataren tsare-tsare na jam’iyyar All Progressives Congress a Kaduna, Kawu Yakassai a ƙaramar hukumar Soba a ranar 25 ga watan Agusta da kuma wani da aka kashe, Adamu Muazu kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene waɗanda aka cafken?

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin a matsayin Bello Suleiman, Ismail Abubakar, Usman Suleiman, Umar Suleiman, da Isah Lawal, dukkansu daga ƙauyen Farin Kasa da ke ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna.

Sauran sun haɗa da Abubakar Bello, Ibrahim Mu’azu da Umar Suleiman.

Hassan ya kuma bayyana cewa, shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutanen, mai suna Hanazuwa, ya tsere amma jami'an tsaro na cigaba da bin sahunsa, yayin da waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Dubun wasu hatsabiban 'yan bindiga 8 da suka addabi mutane ya cika a jihar Kaduna

Hakazalika, kwamishinan ƴan sandan jihar, Musa Garba, ya yabawa jami’an da suka kama waɗanda ake zargin da yin garkuwa da mutanen, inda ya ɗora musu alhakin ma su sanya ido sosai a lokutan bukukuwan da ke tafe.

Sojoji Sun Cafke Shugaban Ƴan Ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar ƴan sandan fararen kaya sun cafke wani shugaban ƴan ta'addan ISWAP.

Jami'an tsaron sun cafke shugaban ƴan ta'addan shi ne yake kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel