Kotu Ta Yanke Mummunan Hukunci Kan Sarkin Fulani da Wasu Mutum 2 Kan Zargin Garkuwa da Mutane

Kotu Ta Yanke Mummunan Hukunci Kan Sarkin Fulani da Wasu Mutum 2 Kan Zargin Garkuwa da Mutane

  • Ado Usman, Sarkin Fulanin Kwara ya gamu da fushin hukuma bayan yanke masa hukuncin daurin rai da rai
  • An yi wa Sarkin Fulanin hukuncin ne tare da wasu mutane biyu kan zargin hadin baki da yin garkuwa da mutane
  • Ana zarginsu da yin garkuwa da wani mai suna Ahmad Abubakar inda su ka karbi naira miliyan daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Babbar kotun jihar Kwara ta yanke hukunci kan Sarkin Fulanin Kwara, Usman Ado daurin rai da rai.

Ana zargin Sarkin Fulanin da wasu mutane biyu kan hada baki da kuma yin garkuwa da mutane, Legit ta tattaro.

Kotu ta daure Sarkin Fulanin Kwara daurin rai da rai kan zargin garkuwa da mutane
Kotu ta yi hukunci kan Sarkin Fulanin Kwara. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

Wadanda ake zargin sun yi garkuwa da wani mai suna Abubakar Ahmad inda su ka karbi kudin fansa naira miliyan daya.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani sun sake Ahmad bayan an biya su kudin fansar da su ka bukata inda ya shafe kwanaki 20 a hannunsu, cewar TVC News.

Har ila yau, wadanda ake zargin sun hada baki ne da wani jami'in soja wanda har yanzu ba a san inda ya ke ba.

Alkaliyar kotun ta nuna takaici kan shugabanni

Yayin hukuncin kotun, Mai Shari'a, Akinpelu Adenike ta ce mutane uku ne su ka hada baki don aikata danyen aikin.

Ta ce maganar su na tare a wurin aikata laifin duk babu wata fa'ida kuma ba za ta hana komai ba.

Akinpelu ta kara da cewa an daura alhakin jama'a ne a kan shugabanni wurin kula da hakkokinsu da ba su tsaro.

Ta ce amma abin takaici su shugabannin ne ke cin amanar talakawansu wurin yin garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Basaraken Abuja zai biya naira miliyan 2 kudin fansar matarsa da aka yi garkuwa da ita

Mutane 8 sun mutu a wani hatsarin mota a Kwara

A wani labarin, wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane takwas tare da raunata da dama a jihar Kwara.

Wannan lamari ya faru ne a kauyen Oke Onigbin da ke karamar hukumar Irepodun da ke jihar.

Wannan na zuwa ne bayan mutane akalla 17 sun mutu yayin da fiye da 50 su ka jikkata a hatsarin mota a jihar Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel