‘Yan Bindiga Sun Yi Barna a Kaduna, Sun Sungume Hakimi a Wasu Sababbin Hare Hare

‘Yan Bindiga Sun Yi Barna a Kaduna, Sun Sungume Hakimi a Wasu Sababbin Hare Hare

  • Har yanzu za a iya cewa ba a kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin Arewa ba, musamman a kewayen jihar Kaduna
  • Kwanan nan wasu miyagun ‘yan bindiga su ka shiga garin Kujama, a nan su ka yi awon gaba da wani basarake da yamma
  • A hanyar Zariya an kai sabon hari a tsakiyar makon nan bayan wasu ‘yan sanda da aka harbe a karamar hukumar Birnin Gwari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Ana fama da matsalar rashin tsaro a wasu yankunan jihar Kaduna, musamman a kwanakin nan da ‘yan bindiga ke ka hare-hare.

Labari ya zo daga Daily Trust cewa ana zargin miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Kujama a karamar Chikun, Steven Ibrahim.

Kara karanta wannan

Wasu sun sace wayar tsohon minista a kotu wajen sauraron shari’ar zabe

‘Yan Bindiga
Jami'an tsaro na fama da ‘Yan Bindiga a Kaduna Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An dauke Steven Ibrahim. Ne tare da wasu mutane biyu yayin da su ke fitowa daga wani wajen shaktawa da ke bayan makarantar Bethel Baptist.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka dauke Mai gari a Kaduna

Mazauna sun shaida cewa abin ya faru ne a kan babban titin Kaduna zuwa garin Kujama a yammacin Lahadin da ta wuce da kimanin karfe 7:00.

Wani jami’in tsaro na sa-kai da aka zanta da shi ya nemi a sakaya sunansa, ya fadawa jaridar cewa ‘yan bindigan sun zo ne dauke da babur.

Zuwansu ke da wuya, sai su ka dauke Mai martaba tare da mutum biyu tare da shi.

'Yan bindiga sun shiga jeji da Mai martaba

Majiyar ta ce mutanen yankin Anguwar Ayaba sun ce sun ga wadannan ‘yan bindiga a lokacin da su ke kokarin shiga cikin daji a kan baburansu.

Kara karanta wannan

Mahara sun bukaci miliyan 53 kudin fansar malamin addini da wasu mutum 2 a jihar Arewa

Da aka tuntubi Ardon Ardodi na garin Chikun, Ibrahim Saleh ya tabbatarwa manema labarai cewa lallai wannan mummunan lamari ya auku.

"Gaskiya ne an yi awon gaba da Mai garinmu. Abin takaici kuma muna fatan Ubangiji ya kawo karshen wadannan abubuwa.”

- Ibrahim Saleh

'Yan bindiga sun kai hari a Birnin Gwari

Ana haka sai ga labari cewa wasu ‘yan sanda biyu sun samu rauni yayin da ‘yan bindiga su ka kai hari a kauyen Kakangi a Birnin Gwari.

Shugaban wata kungiya ta mutanne garin na Birnin Gwari, Ishaq Kasai ya ce abin ya faru ne da ‘yan sanda su ka hana ‘yan bindiga yin ta’adi.

...an yi garkuwa da wani daga Zaria

A daren yau Alhamis, Legit ta samu labarin wani hari da ake zargin ‘yan bindiga sun kai a yankin Likoro, inda su ka nemi dauke Bayin Allah.

Wasu daga cikin manoma daga garin Zariya da aka kai wa harin sun kubuta, amma miyagun sun dauke wani wanda yanzu ya na hannunsu.

Kara karanta wannan

Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan motocin 'yan ta'adda a Borno

"Abin ya yi kamari" - Ribadu

Malam Nuhu Ribadu ya fadawa sojoji cewa ana fuskantar cikas sosai a wajen kasafin kudi saboda halin da aka mika masu mulki a watan Mayu.

An rahoto mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaron ya na cewa sun gaji kasa mai wahalar sha’ani kum a tsiyace saboda tulin bashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel