Gwamna Namadi Ya Faɗi Matsaloli 2 da Suka Fara Takurawa Mutane a Jihar Jigawa

Gwamna Namadi Ya Faɗi Matsaloli 2 da Suka Fara Takurawa Mutane a Jihar Jigawa

  • Gwamna Namadi na jihar Jigawa ya nuna damuwa kan yadda lamarin garkuwa da mutane ke karuwa duk mako a jihar
  • Yayin da ya karɓi bakuncin sabon kwamishinan ƴan sandan Jigawa, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba zata lamurci lalacewar tsaron a'umma ba
  • Umar Namadi ya faɗa wa kwamishinan cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen tallafa musu domin sauƙaƙa aikin jami'an tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi Ɗan Modi na jihar Jigawa ya koka kan yawaitar faruwar kes ɗin garkuwa da mutane a faɗin jihar da ke Arewa maso Yamma.

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi.
Gwamna Dan Modi Ya Koka Kan Yawaitar Garkuwa ada Mutane a Jihar Jigawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi baƙuncin sabon kwamishinan 'yan sanda da aka turo jihar, Ahmadu Abdullahi, a gidan gwamnati da ke Dutse.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Ɗan Modi ya bayyana cewa a kowane mako sai an samu rahoton kai harin garkuwa da mutane a wasu sassan jihar Jigawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Gwamna Umar Namadi ya ce:

"A cikin makonni biyu da suka gabata, bana jin daɗin halin rashin tsaron jihar nan, mutum biyu aka yi garkuwa da su ciki mako ɗaya, ba zan lamurci faruwar irin haka ba."
"Akwai bukatar mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu yi aiki tare wajen kawo karshen garkuwa da mutane. Haka nan kes ɗin fashi da makami na ƙaruwa a jihar nan."
"Ya zama wajibi jami'an yan sanda su zage dantse su yi aiki tukuru tun daga matakin ƙasa zuwa hedkwatar jiha, sha'anin tsaro ya shafi kowa da kowa."

Gwamnatin Jigawa zata taimakawa jami'an tsaro

Gwamna Namadi ya ƙara da cewa gwamnatinsa zata taimaka wa jami'an tsaro da kayan aikin da suke buƙata domin saukaka musu aikinsu na tsare al'umma.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024

"Batun tsaro ya shafi kowa, a matsayin mu na gwamnati zamu baku duk haɗin kan da kuke buƙata wajen tabbatar da kun sauke nauyin da ya rataya a wuyanku," Gwamnan ya faɗawa CP.

Wani mazaunin ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Aminu Majeh, ya shaida wa Legit Hausa cewa duk da an san Jigawa da zaman lafiya, ya kamata a magance irin waɗannan matsalolin.

A cewarsa, mafi yawan halin rashin tsaron da ake ciki a arewacin Najeriya daga wani abu ne kalilan da aka raina, sai ya girma ya zama babba.

Majeh ya ce:

"Gaskiya muna yi wa Ɗanmodi fatan alheri amma wannan matsalar ta garkuwa da muke jin labarin ta shigo Jigawa, ya kamata a tashi tsaye a kawar da ita."
"Wata matsalar daga ƙanƙanin abu take zama babba, bamu fatan lamarin ya gurma ya fi karfin Gwamnati, Allah ya kawo mana karshen abun a ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Hatsarin mota ya kashe mutane 11

A wani rahoton na daban An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kebbi wanda ya salwantar da rayukan mutum 11.

Hatsarin motar wanda ya ritsa da wata motar tirela mai ɗauke da kayayyaki da fasinjoji ya kuma yi sanadiyyar jikkata mutum 54.

Asali: Legit.ng

Online view pixel