Kaico: An Cafke Yan Jami'an Yan Sanda Bisa Laifin Yin Garkuwa da Mutane da Neman Kudin Fansa

Kaico: An Cafke Yan Jami'an Yan Sanda Bisa Laifin Yin Garkuwa da Mutane da Neman Kudin Fansa

  • Wasu jami'an ƴan sandan jihar Rivers sun shiga hannu bisa zargin sace wani matashi da neman kuɗin fansa
  • Jami'an ƴan sandan dai sun sace matashin ne wanda yake aiki a wani otel lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki
  • Wani jami'in ƴan sanda mai muƙamin DPO ne ya yi musu shigo-shigo ba zurfi ya cafke su domin fuskantar hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - An cafke jami'an ƴan sanda da ba a bayyana adadinsu ba a jihar Rivers bisa laifin sace ma’aikacin wani otel tare da neman a biya su Naira miliyan ɗaya domin su sako shi.

Wanda aka yi garkuwa da shi ɗin ma’aikacin wani otal ne a birnin Port Harcourt, lokacin da yake a kan hanyarsa ta zuwa aiki da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Juma'a, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP sun halaka yan sakai 2 a yayin wani farmaki

An cafke yan sanda a Rivers
An cafke yan sandan ne kan zargin sace wani matashi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An tattaro daga wata majiya mai tushe da ke kusa da rundunar ƴan sandan Rivers cewa jami’an ƴan sandan sun tare ma'aikacin ne a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki, inda suka bincike jikinsa ba tare da samun wani abun laifi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba su gamsu ba, sai jami'an ƴan sandan suka buɗe wayarsa, inda nan ma ba su samu wani abun laifi ba.

Sai dai, majiyar ya bayyana cewa a lokacin da suke duba wayarsa, ƴan sandan sun gano inda yake aiki inda nan take suka yi garkuwa da shi.

Daga nan sai suka tilasta shi ya kira ƴan uwansa domin su biya naira miliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa domin belinsa a hannunsu.

Wacce hanya aka bi wajen cafke ƴan sandan?

"Sun tilasta masa ya kira maigidansa, mamallakin otel ɗin a Choba. Lokacin sa aka kira shi, sai ya yi hikimar kiran wani DPO wanda ya nuna shi mahaifinsa." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sheke yan bindiga 50 a yayin wani artabu

"Jami'an ƴan sandan bisa rashin sani suka fara cinikin kuɗin fansa da DPO (wanda aka sakaya sunansa) ta wayar matashin suna tunanin cewa shi ne mahaifinsa."

DPO na ƴan sandan ya ɗauki mutanensa zuwa dajin Aluu inda suka tsare matashin, suna jiran a kawo musu kuɗin fansa.

Nan da nan aka ƙwace makaman da ke hannunsu tare da cafke su. Abin mamakin shi ne sun fito ne daga ofishin ƴan sanda na yankin Borokiri a birnin Port Harcourt.

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, rundunar ƴan sandan jihar Rivers ba ta fitar da wannan labarin ba.

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Ƴan Bindiga 50

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƴan sakai da sojoji sun sheƙe ƴan bindiga 50 a jihar Taraba.

Jami'an ƴan sandan sun sheƙe ƴan bindigan ne a yayin wani artabu da suka yi ƙaramar hukumar Bali ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel