Masu Garkuwa Sun Rike Basaraken Abuja da Yayansa 3, Sun Sako Matarsa Don Nemo Kudin Fansa

Masu Garkuwa Sun Rike Basaraken Abuja da Yayansa 3, Sun Sako Matarsa Don Nemo Kudin Fansa

  • Rahotanni na nuni da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sako matar wani basarake don nemo kudin fansar mijinta da 'yayansu uku
  • A ranar Larabar makon da ya gabata ne masu garkuwar suka sace basaraken a garin Mpape, karamar hukumar Bwari, Abuja
  • Sai dai matar da suka sako, ta ce ba ta san inda za ta samo naira miliyan dari don fansar mijinta da 'yayanta ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bwari, Abuja - Masu garkuwa sun sako daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su daga wata anguwar GRA a Mpape, karamar hukumar Bwari, Abuja a makon da ya gabata.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne masu garkuwan suka sako wacce suka kamar domin nemo kudin fansar sauran mutanen da ke tsare a hannun su.

Kara karanta wannan

Alkalluma: Yan Najeriya miliyan 1.8 na dauke da cutar kanjamau, Majalisar Tarayya ta dauki mataki

Rundunar 'yan sanda/Garkuwa da mutane/Birnin tarayya Abuja
Sai dai matar da suka sako, ta ce ba ta san inda za ta samo N100m don fansar mijinta da 'yayan ba. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Wacce suka saki, Aisha Peter , wacce mata ce ga basaraken garin, Dabod Pter, ta ce masu garkuwan sun kai ta har babban titi, tare da ba ta kudin motar komawa gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwa sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa

A iya nazarin ta, tana hasashen mabuyar masu garkuwan a Kaduna ne, la'akari da tafiyar kasa da ta sha tun daga mabuyarsu zuwa titi, kamar yadda ta shaidawa City & Crime.

Ta bayyana cewa:

"Sun nemi na kawo kudin fansar mijina har naira miliyan hamsin, sai kuma naira miliyan hamsin ta fansar 'yayana guda uku.
"Sun bani wa'adin mako biyu na hada kudin na kai masu ko kuma su dauki iyalina su mayar da su zuwa babban sansanin su da ke jihar Zamfara."

Sai dai, Aisha ta ce ba ta san inda za ta nemo wadannan makudan kudade ba.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya dira kan mata da ke hana mazajensu hakkin kwanciyar aure, ya fadi halayensu

Yunkurin kisan kai: An tsare basarake da mutum 14 a Oyo

A wani labarin, kun ji cewa wata babbar kotun jiha a Oyo mai zamanta a Ogbomoso, ta bayar da ajiyar mai sarautar Oloko na Oko, a karamar hukumar Surulere ta jihar.

Kotun ta garkame basaraken mai suna Oba Solomon Akinola tare da wasu mutane 14 a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, bisa laifin kwacen fili da yunkurin kisa, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel