Masu Garkuwa Da Mutane
Wani ma’aikacin hukumar INEC da aka yi ram da shi a ranar jaji-birin zaben Gwamnonin jihohi, ya samu ‘yanci. Sanarwa ta fito daga INEC cewa malamin zaben ya tsira.
Jami'an tsaro na ƴan sakai sun samu nasarar halaka masu garkuwa da mutane mutum huɗu a wani artabu da suka yi a jihar Kebbi bayan sun kai musu sumame.
Idan manomi ya yi sa'a gonarsa ta yi kyau, sai ya biya kusan N100, 000 kafin ya yi girbi. ‘Yan bindiga na karba a hannun manoma kafin a cire kayan gona a Kaduna.
Kwanaki kadan bayan sace mutanen a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, wasu daga cikin jariran guda biyar sun mutu yayin da su ke hannun 'yan bindiga.
Dillalan kasuwar shanu a jihar Abia sun zargi gwamnatin jihar da mu su sharri don samun damar korarsu a jihar gaba daya, sun karyata samun gawarwarki a kasuwar.
Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wani mai sarautar gargajiya tare da sace matarsa da dansa da kuma wasu mutane takwas a kauyukan da ke makwabtaka da su.
Rundunar sojoji a jihar Kebbi ta yi ajalin wani kasurgumi kuma kwamandan 'yan bindiga, Mainasara da wasu biyu a jihar Kebbi a wani mummunan hari da ta kai.
Ana zargin 'yan bindiga sun fille kan wani babban dan sanda a jihar Abia bayan sun farmaki rundunar, sai dai rundunar ta musanta inda ta ce dan sa kai aka kashe.
Rundunar sojin Najeriya ta yi ajalin mayakan Boko Haram 6 a jihar Yobe yayin ta cafke wasu mutane biyu da ke safarar miyagun makamai a jihar Kaduna.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari