Babbar Nasara: An Kashe Gawurtaccen Ɗan Bindiga da Ya Hana Jama'a Zaman Lafiya a Arewa

Babbar Nasara: An Kashe Gawurtaccen Ɗan Bindiga da Ya Hana Jama'a Zaman Lafiya a Arewa

  • Jami'an tsaro yan banga sun halaka ƙasurgumin ɗan garkuwa da mutane, Dogo Oro, a jihar Kebbi ranar Jumu'a
  • Sakataren watsa labaran Kauran Gwandu, Ahmed Idris, ya ce ɗan ta'addan ya jima yana takura wa al'umma a kananan hukumomi biyu
  • Ya yabawa gwamnan jihar bisa yadda yake bada goyon baya ba tare da gajiya ba wajen ganin mutane sun samu tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Gawurtaccen ɗan bindigan nan mai garkuwa da mutane, Dogo Oro, ya baƙunci lahira a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gwamnatin jihar Kebbi karƙashin Gwamna Nasiru Idris Ƙauran Gwandu ce ta tabbatar da mutuwarsa ranar Jumu'a, 1 ga watan Disamba, 2023, Channels tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya buƙaci mataimakin gwamnan APC ya sa hannu a takardar murabus kan abu 1 tal

An kasurgumin ɗan bindiga a Kebbi.
Kasurgumin Mai Garkuwa da Mautane, Dogo Oro, Ya Bakunci Lahira a Jihar Kebbi Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Yan banga ne suka yi nasarar halaka shi a ƙauyen Tunga da ke ƙaramar hukumar Bunza, in ji Ahmed Idris, sakataren watsa labaran Gwamna Nasiru Idris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe Dogo Oro

Ya bayyana cewa ɗan bindigan ya kai hari tare da buɗe wa mutane wuta masu ɗauke da kwari da baka a ɗaya daga cikin kauyukan da suka kewaye Kanzanna ranar Jumu'a.

A sanarwan da ya fitar, hadimin gwamnan ya ce:

"Rahoton ci gaban da aka samu a sha'anin tsaro ya nuna cewa ranar 1 ga watan Disamba, 2023, jami'an tsaron mu yan sa'kai sun halaka wani ƙasurgumin mai garkuwa da ake kira Dogo Oro."
"Oro ya yi kaurin suna wajen aikata muggan ayyukan ta'addanci a kananan hukumomin Bunza da Kalgo, kuma jami'an mu yan banga sun kashe shi da safiyar nan a garin Tunga."

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Ahmed Idris ya ƙara da cewa ɗan bindigan ya jima yana farmakan mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, cewar rahoton Tribune.

Ya ce bisa nasarar da ‘yan banga suka samu, yanzu mazauna yankunan za su samu damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da cikas ba, kuma cikin tsaro.

Ya yabawa gwamna bisa irin goyon bayan da yake baiwa jami'an tsaro domin kawo karshen dukkan wani kalubalen tsaro a jihar Kebbi.

An kama yan bindiga 8 a Kaduna

A wani rahoton kuma Yan sanda sun kama yan bindiga takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a sassa daban-daban na jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya faɗi sunayen waɗanda aka kama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel