Masu Garkuwa Da Mutane
Mutane a wasu yankuna na jihar Zamfara musamman karamar hukumar Kaura na Moda na barin gidajensu da dare su dare da safe saboda tsaron hare hare.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargin iyalan dan bindiga Ado Aliero ne a garin Madina yayin da suka tafi aikin Hajji daga Najeriya.
DSS ta kama Sani Galadi a Sokoto yana kokarin tafiya aikin Hajji. Ana zargin Galadi da garkuwa da mutane a Zamfara, kuma yanzu haka yana hannun DSS domin bincike.
Jami'an DSS sun kama Yahaya Zango, hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin alhazai na Abuja. Jama’a na tambaya: me zai faɗa wa Allah kan ta'addancinsa?
Jami'an tsaro sun kama wani da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane a sansanin aikin Hajji da ke Abuja yayin da ake tantance maniyyata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace basarakena jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, ƴan sanda sun fara farautarsu domin ceto shi.
'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun daure mutane 2 da suka je daji karbo shugaban APC da aka yi garkuwa da shi. Mutanen sun kai kudin fansa amma aka rike su.
Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin Gwamna Monday Okpebholo ya rusa wani gida da wasu masu garkuwa suke amfani da shi a Benin City, ta kama miyagun.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa DSS kan kama masu garkuwar da suka sace yarinya mai shekara 1 suka wurga ta rijiya bayan karbar kudin fansa.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari