Lokaci Ya Yi: An Yi Jana'izar Basaraken 'Yan Bindiga Suka Kashe a Jihar Sakkwato
- Rahotanni sun nuna cewa an yi jana'izar mutanen da yan bindiga suka kashe a kauyukan Kulodo da Kwamtsi da ke jihar Sakkwato
- Daga cikin wadanda suka rasa ransu a harin yan ta'addan har da magajin garin Kulodo da ke karamar hukumar Bodinga
- Mazauna sun bayyana marigayi magajin garin a matsayin shugaba mai mutunci wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'ummarsa hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - An yi jana'izar magajin garin Kulodo, babban dansa da wasu mutum hudu da aka kashe yayin harin 'yan bindiga a kauyukan Kulodo da Kwamtsi da ke karamar hukumar Bodinga a Jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa mutum biyar ne aka kashe a kauyen Kulodo, yayin da aka kashe mutum guda a kauyen Kwamtsi da ke makwabtaka da shi.

Kara karanta wannan
Mutanen da 'yan bindiga suka sace a wurin Ibada sun dawo gida, mutum 1 ya mutu a Ekiti

Source: Original
Baya ga haka, an yi garkuwa da mutum hudu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka sakamakon harin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda aka dauko gawar basaraken
Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis, amma ba a samu damar kwashe gawarwakin wadanda aka kashe ba sai da yammacin ranar Juma'a.
Sun ce hakan ya faru ne saboda fargabar cewa maharan na ci gaba da fakewa a yankin da nufin sake dawowa.
Sai bayan jami'an tsaro da manyan jami'an gwamnati sun isa kauyukan ne aka samu damar dauko gawarwakin tare da yi musu jana'iza.
Red Cross ta taimaka wajen jana'izar
Jami'in kungiyar agaji ta Red Cross, Ahmad Suleiman, ya tabbatar cewa masu aikin sa-kai na kungiyar sun hada hannu da jami'an tsaro da mazauna yankin wajen dauko gawarwakin, shirya jana'iza da kuma binne mamatan bisa koyarwar addinin Musulunci.
Bayan jana'izar, an ga jami'in Red Cross din yana tattaunawa da mazauna yankin, wadanda suka bayyana harin a matsayin abin takaici da firgici.
Yadda yan bindiga suna kewaye kauyuka
Wani mazaunin yankin ya ce kimanin 'yan bindiga 150 ne suka mamaye kauyukan, inda kowane babur ke dauke da mutum biyu zuwa uku masu dauke da makamai.
Ya ce:
"Sun kewaye kauyukanmu suna harbe-harbe ba kakkautawa, sannan suka rika shiga gidaje da shaguna. Sun kwashe fiye da dabbobi 200 tare da wawashe dukiyoyin jama'a."
Ya kara da cewa yawancin wadanda aka kashe an harbe su ne a cikin gidajensu yayin da suke kokarin buya.
A cewarsa, magajin garin Kulodo da babban dansa sun rasa rayukansu ne a kofar gidansu yayin da suke kokarin tserewa daga maharan.
Ya bayyana marigayi magajin garin a matsayin shugaba mai mutunci wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'ummarsa hidima.
An yi zanga-zanga kan tsaro a Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa mutanen yankin karamar hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato sun harzuka kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen da suka tsere daga ƙauyukansu sakamakon matsalar tsaro sun gudanar da zanga-zanga ranar Juma'a da ta wuce.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce zanga-zangar na da nufin jawo hankalin gwamnati kan tabarbarewar matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng
