Jami’in Bankin Duniya Ya Fadi Babbar Matsalar da ke Damun Najeriya
- Bankin duniya ya kore tsoron da ake ji game da yawan bashin da ake cewa yana kan wuyan Gwamnatin Najeriya
- Mathew Verghis ya ce abin da ya kamata kasar ta damu da shi, shi ne yadda kudi za su rika shigo mata cikin asusunta
- Darektan na bankin duniya ya alakanta cigaban da ake samu a kasashe da kudin da ake karbowa sai a biya daga baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mathew Verghis wanda shi ne Darektan bankin duniya a Najeriya bai ganin cewa bashin da ake bin kasar ne babban kalubalenta.
Duk da yadda ake kuka da yadda Najeriya ta ke yawan cin bashi, Mathew Verghis yana ganin akwai matsalolin tattalin da suka sha gaban wannan.

Source: Getty Images
Mace ce babbar matsalar tattalin arzikin Najeriya?
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels, Mista Mathew Verghis ya ce babban matsalar tattalin arzikin Najeriya ita ce rashin kudin shiga.
Babban jami’in na bankin duniya yana ganin kudin shigan da kasar Afrikar ta ke samu yayi kadan idan aka kamanta da girman tattalin arzikinta.
“Daga nazarinmu, Najeriya ba ta da matsalar yawan bashi, tana da matsalar karincin kudin shiga ne,”
Ya ce sauran sa’annin Najeriya sun sha gabanta idan ana zancen kudin shiga kuma har a wajen bashi, sauran kasashe sun fi ta karbo aron kudi.
Masanin tattalin ya kawo misali da kasar Ghana wanda gwamnatinta ta ke fama da matsalar bashi. The Cable ta fitar da labarin a yammacin Juma'a.

Source: Getty Images
Bankin duniya ya bada shawarar a ci bashi
Idan ana so a gudanar da wasu ayyukan da za a ga fa’idarsu nan gaba, Verghis ya ce dole ne sai kasashe sun rika cin bashin kudi, su biya daga baya.
Ta hanyar karbo aro ne ya ce za a samu sauyin rayuwa da kuma bunkasar tattalin arzikin kasashe.
"Najeriya tana cin bashi ne saboda dalilan da suka sa duka sauran kasashe suke karbo aron kudi.
Idan kana son ganin sakamako, ana son a yi wa mutane aiki, to kudin da ake samu a shekera-shekara ba zai isa ba.
Saboda haka sai a karbo aro, a samu nasara, wannan zai bada damar samun karfin biyan bashin”
Bukatar Gwamnatin Najeriya ta dage da kudin shiga
A kokarinsa na zama lauyan cin bashi, Vanguard ta rahoto shi yana bada misali da karbo aron kudi da nufin a inganta harkar wutar lantarki a Najeriya.
Maimakon a yi ta kuka da yawan bashi, Verghis ya bukaci a duba yadda kudi za su shigo lalita, yake cewa wannan ita ce babbar barazana ga tattali.
Darektan bankin duniyan na Najeriya ya ce idan kuma ana so a iya biyan bashin da ake bin Najeriya dole ne a nemo hanyoyin samun kudin shiga.
Ministan Najeriya ya canza magana bayan shan korafi
Maganar Ministan matasa ta rikide da surutu ya yi yawa a kan canza khakin NYSC zuwa atamfa kamar yadda labari ya zo a kwanakin baya.
Ministan ya karyata cewa za a kyale khaki a koma sa atamfa a NYSC, ya ce misali ya kawo amma ba a kai ga amincewa da wani tufafi ba.
Ayodele Olawande Wisdom ya yi karin hasken ne bayan wasu sauyi da Gwamnatin Najeriya ta yi wa tsarin NYSC bayan shekaru kimanin 50.
Asali: Legit.ng

