Matakin Gwamna Abba Ya Daga Darajar Kano, Ta Hau Matsayi na 1 a Jerin Jihohin Kasashe 15

Matakin Gwamna Abba Ya Daga Darajar Kano, Ta Hau Matsayi na 1 a Jerin Jihohin Kasashe 15

  • Jihar Kano ta zama ta farko a jihohin da ke kasashen kungiyar ECOWAS wajen kashe kudi a fannin inganta harkokin ilimi
  • Rahoton Jami'ar Paris ya ba Kano maki 87.21 a jadawalin kashe kudin ilimi, lamarin da ya sa ta yi fice a kasahen Yammacin Afirka
  • An danganta nasarar da karin kasafin ilimi da kyakkyawan aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin mai ci karkashin Gwamna Abba Kabir

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jihar Kano ta zama gwamnatin jiha mafi taka rawar gani a kasashen kungiyar ECOWAS wajen kashe kudade a fannin ilimi.

Hakan dai na kunshe ne a rahoton 2026 Sub-National Education Spending Index da Jami'ar Paris ta fitar.

Gwamna.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wani taro da aka shirya a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa wannan rahoto a shafinsa na Facebook

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Kano ta shiga gaban jihohin ECOWAS

Rahoton ya sanya Kano a matsayi na farko cikin gwamnatocin jihohi da yankuna 209 a kasashe 15 mambobin kungiya raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka watau ECOWAS.

A cewar rahoton, Kano ta samu maki 87.21 a jadawalin S-WAESI, inda ta zarce Dakar da Saint-Louis na kasar Senegal.

Jihar Legas ce ta zo ta biyu daga Najeriya, inda ta kasance a matsayi na 16 a jerin gaba daya.

Yadda aka tantance jihohin ECOWAS

Rahoton ya yi amfani da wasu ma'auni wajen tantance yadda gwamnatoci jihohi ke bai wa ilimi muhimmanci, wanda ya kunshi adadin kudin da aka kashe a ilimi, kudin da ake kashewa kan kowane dalibi, yadda ake aiwatar da kasafin kudi da sauransu.

Rahoton ya ce Kano ta samu wannan matsayi ne saboda yawan kudin da take warewa ilimi da kuma yadda take aiwatar da kasafinta yadda ya kamata.

Dokar ta baci a fannin ilimi a Kano

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m

Rahoton ya zo ne bayan gwamnatin Jihar Kano ta ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi domin magance matsalolin da suka dade suna addabar makarantu, ciki har da lalacewar gine-gine da tabarbarewar yanayin koyarwa.

Tun bayan wannan mataki, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da ware kaso mai yawa na kasafin kudinta ga bangaren ilimi.

An karkata kudaden wajen ginawa da gyaran makarantu, daukar sababbin malamai, samar da kayan koyarwa da kuma fadada damar samun ingantaccen ilimi a fadin jihar.

Abba.
Dakin taron kungiyar ECOWAS da Gwamna Baba Kabir Yusuf na Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Da take martani, hukumar K-SAFE mai kula da harkokin ilimi a Kano ta ce wannan nasara ta nuna yadda gwamnatin jihar ke da cikakken kudurin inganta ilimi, bunkasa ababen more rayuwa a makarantu.

Tribune Nigeria ta rahoto cewa masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun bayyana rahoton a matsayin tabbacin cewa sauye-sauyen da gwamnatin jihar ta fara bayan ayyana dokar ta-baci sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Gwamna Abba ya yi garambawul a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sauye-sauyen masu ba shi shawara domin inganta aiki a gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan

DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

Haka kuma gwamnan ya amince da waɗansu sababbin nade-naden domin karfafa tsarin mulki da inganta ayyukan gwamnati.

Ya kuma soke ofisoshin mai ba gwamna shawara kan harkokin cikin gida na gidan gwamnati da kuma mai ba da shawara kan ofisoshin hulda da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262