Gwamna Ya Tura Motocin Buldoza, An Rusa Wani Babban Gida da Ake Aikata ba Daidai ba

Gwamna Ya Tura Motocin Buldoza, An Rusa Wani Babban Gida da Ake Aikata ba Daidai ba

  • Gwamnatin Edo ta rusa wani gida da aka gano masu garkuwa da mutane na amfani da shi wajen aikata miyagun laifuffuka a Benin
  • Rahoto ya nuna cewa an kai gidan ƙasa ne bayan kama masu garkuwa da mutane ciki har da ɗan uwan mai gidan
  • Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya ce gidan na wata yar uwarsa ne da ke zaune a ƙasar waje, ta ba shi yake kulawa da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamnatin Jihar Edo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Monday Okpebholo ta rusa wani gida da ake alakanta shi da wata tawagar masu garkuwa da mutane da ke aikata laifuka a Benin.

Gidan, wanda wata mata da ke zaune a kasar Italiya ta mallaka, ana zargin cewa dan uwanta, Osamede Asemota, ne yake amfani da shi wajen aikata miyagun laifuffuka.

Gwamna Monday Okpebholo.
Gwamnatin Edo ta rusa gidan da aka gano yana da alaƙa da miyagu a Benin Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Leadership ta tattaro cewa Asemota, na ɗaya daga cikin shugabannin tawagar ƴan bindigar da ke sace mutane kuma suna amfani da gidan wajen tsara ayyukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa gwamnatin Edo ta rusa gidan?

Gwamnatin Edo ta ruguza gidan ne bayan an kama Asemota, kuma ya kwararo bayanai tare da amsa cewa yana daga cikin masu sace mutane a Benin.

Duk da matar da ta mallaki gidan ba ta da masaniya kan ayyukan laifin da dan uwanta ke aikatawa, gwamnatin jihar ta dauki matakin rushe gidan don cika alkawarinta.

Idan ba ku manta ba Gwamna Okpebholo ya sha alwashin rusa duk wani gida da aka gano yana da alaƙa da miyagun da suka hana jama'a zaman lafiya.

Miyagun da aka kama sun bada bayani

Asemota, wanda ke hannun hukuma yanzu, ya ce a aikin garkuwa da suka yi na ƙarshe kafin damƙe shi, ya samu kudi N350,000.

Ya ce ya samu kuɗin ne bayan sace wata mata daga shagonta a tashar Ramat Park da ke Benin City.

"Mun sace matar ne a shagonta a tashar Ramat, muka kai ta cikin daji kusa da tashar Agbor. Na zauna da ita a dajin na tsawon kwana biyu, daga baya abokaina suka kawo min rabona na kudin fansa,” inji shi.
Jihar Edo.
Gwamnan Edo ya sha alwashin dawo da zaman lafiya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ya kuma ce tawagarsu ta mutane biyar suna da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da dama a yankunan Aduwawa, Eyaen da Auchi Bypass.

Asemota ya ce yana jin kunya da bakin ciki kan amfani da dukiyar 'yar uwarsa cikin irin wannan aika-aika, yana mai cewa:

“Ina jin bakin ciki da rudani. Ban san yadda za ta ji idan ta ji wannan labarin ba, domin ta kasance mai taimakon rayuwata.”

Yadda masu garkuwa ke raba kuɗin fansa

Haka nan ɗaya daga cikin ƴan tawagar Asemota, Michael Tare, ya bayyana cewa ya samu Naira miliyan daya a matsayin rabonsa daga sace wannan mata.

Ya ce bayan ya gudu zuwa Jihar Delta da kudin, daga baya ya dawo Benin saboda kwaɗayi, wanda hakan ne ya sa aka cafke shi.

Gwamnan Edo ya dakatar da basarake

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya dakatar da Sarkin Uwano, George Egabor na ƙaruwar sace-sacen mutane a yankinsa.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya lashi takobin ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka gano yana da hannu a lamarin rashin tsaron jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da aikata miyagu ayyuka a jihar ba domin ya shirya kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262