Masu Garkuwa Da Mutane
Rahotanni sun bayyana yadda babban jigo a jam'iyyar APC, Rauf Adeniji ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane, bayan sace shi a watan Janairun shekarar 2025.
Rundunar 'yan sanda ta ceto mutane 17 da aka sace a jihar Kaduna tare da kwato manyan bindigogi har 21 a cikin wata motar haya. Sun gwabza fada da yan fashi.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dauki matakin rufe hedkwatarta ta kasa har na tsawon wani lokaci. APC ta dauki matakin ne kan kisan da aka yi wa daraktan ta.
Jami'an tsaro sun yi nasara a kan wasu miyagun 'yan ta'adda da suka kutsa kauyen Mahume dake Dandume a jihar Katsina, tare da sace mutane shida daga gidajensu.
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang ya bayyana cewa mutanensa suna cikin mawuyacin hali yayin da fitinannun 'yan bindiga suka mamaye garurwa akalla 64.
A Kaduna, 'yan bindiga sun sace Fasto Samson Ndah Ali daga gidansa a Mararaba Abro. Sojoji da 'yan sanda sun bi sahun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Dakarun rundunar 'yan sanda sun ceto mata 5 a Kankara da wasu 2 a Malumfashi da ke jihar Katsina bayan fafatawa da ‘yan bindiga, an mayar da su gida lafiya lau.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci iyalan da mutanen da 'yan bindiga suka sace kan su daina biyan kudaden fansa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace Blessing Adagba, mai taimakawa Gwamnan Ebonyi, a unguwar Okposhi Eheku da ke karamar hukumar Ohaukwu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari