Manyan Labarai A Yau
A ‘yan kwanakin nan, ‘Yan ta’adda na kokarin karbe iko da wasu garuruwa. Yau aka ji ‘Yan Islamic State in West Africa Province sun tare motocin abinci a Borno.
Bisa dukkan alamu Yusuf Datti Baba Ahmed ne zai zama ‘Dan takaran Mataimakin Shugaban kasa a jam'iyyar LP. A saurari sanarwar da za a fitar nan da an jima.
Wani mummunan hatsarin mota ya afku a garin Kano inda ya yi sanadiyar mutuwar Khadija da Rasheeda yayin da suke hanyar dawowa daga cefanen bikin babban Sallah.
Alkalin kotun laifuka na musamman, Justis Oluwatoyin Taiwo, ya yankewa Bolarinwa Abiodun, wani janar din soja na bogi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan Reverend Daniel Umaru na Cocin EYN da ke Njairi a karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa, inda suka kashe ‘ya’yansa maza.
Peter Obi ya sharara karya game da kwangilar Siemens. Hadimin shugaba Muhammadu Buhari ya zargi ‘dan takaran shugaban kasa da yi wa mutane karya kwanan nan.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da 'yan Boko Haram suka kai kan gidan gyara hali na Kuje.
An kara tsaurara matakan tsaro a garuruwan da ke yankin Kuje da kewaye a babbar birnin tarayya, Abuja bayan farmakin da yan Boko Haram suka kai kurkukun Kuje.
Matuka Keke Napep sun fadawa Bola Tinubu a takarda cewa babu wanda ya kamata ya dauka irin Buba Marwa, an nemi ayi na’am da takarar Tinubu-Marwa a zaben 2023.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari