Karar kwana: Yadda wasu matan aure suka rasu a hadarin mota yayin da suke dawowa daga cefanen sallah

Karar kwana: Yadda wasu matan aure suka rasu a hadarin mota yayin da suke dawowa daga cefanen sallah

  • Allah ya yiwa wasu matan aure biyu rasuwa sakamakon hatsarin mota a cikin babban birnin jihar Kano
  • Khadijah da Rasheeda wadanda ke aure yaya da kani sun je kasuwa don cefanen Sallah ne inda suka hadu da ajalinsu
  • Motarsu ta ci karo da wani babban icce bayan sun yi kokarin kaucewa wata mota da ta tunkaro su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Wani mummunan hatsarin mota ya afku a garin Kano inda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata biyu yayin da suke dawowa daga cefanen bikin babban Sallah.

An tattaro cewa motar mamatan Khadija da Rasheeda wadanda ke auren yaya da kani wato Nura Garba Khalil da Adamu Garba Khalil ya kwace masu inda suka je suka bigi wani icce bayan wata mota ta kauto zuwa inda suke.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Laraba a hanyar gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Tawagar shugaban kasa basu tabuka komai ba a lokacin da yan bindiga suka auka masu – Mazauna kauyukan Katsina

Jihar Kano
Karar kwana: Yadda wasu matan aure suka rasu a hadarin mota yayin da suke dawowa daga cefanen sallah Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Nura ya ce matan nasu sun hadu da ajalinsu ne lokacin da wata mota ta tunkaro hanyarsu sannan suka yi kokarin kaucewa amma sai suka bigi icce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Bana wajen da hatsarin ya afku amma an sanar da ni cewa wani direba ne ya kusan buge motarsu. Don haka, ka san a matsayinta na mace, ta yi kokarin kaucewa sai motar ta bar hanya sannan ta daki icce.”

Wani ganau, wanda ya bayyana kansa a matsayin Badamasi, ya fada ma Daily Trust cewa motar ta bar hanya sannan ta daki icce a hanyar gidan gwamnati.

Badamasi mai siyar da fetur kusa da inda abun ya faru ya ce:

“Daya daga cikinsu ta mutu ne a nan take yayin da aka kwashi dayar zuwa asibiti da ranta. Babu mota a kusa da su ta gaba ko baya, motarsu dai ta hade da icce ne.”

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

Nura Garba Khalil ya bayyana matayen nasu a matsayin aminai, yana mai cewa “sun je kasuwa ne don yowa iyalin cefanen sallah.

Ya ce:

“Na firgita sosai. Kawai dai abun da zan iya yi shine rokon Allah ya gafarta masu kuma zan yi kokarin ganin na yi hakuri. Muna iya samun sabani da matata amma muna sulhu a tsakaninmu ba tare da mun sako iyayen kowannenmu ba.”

Khadija ta bar yara uku yayin da Rasheeda ta bar yara hudu.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), AA Labaran, ya ce zai yi jawabi yadda ya kamata bayan bincike daga ofishin da ya dace a FRSC.

Mummunar gobara ta lashe rayukan ma'auratan likitoci a Maiduguri

A wani labari na daban, mun ji cewa gobara ta lakume rayukan wasu ma’auratan likitoci, Dr Auta Gidado da matarsa Dr Amina Ahmad.

Har zuwa mutuwarsu, su dukka suna aiki ne a karkashin asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Majiyoyi: Dalilin da yasa maharan jirgin kasan Kaduna suka farmaki magarkamar Kuje

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a safiyar Lahadi a gidansu da ke Lagos Street, Maiduguri, kuma ana zaton fetur ne ya haddasa gobarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel