Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin

Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin

  • Rashin kafa wani tsari na doka da zai bayar da fifiko wajen kamawa da hukunta masu laifi shine ke kara tabarbarar da lamarin tsaro a kasar nan
  • Wannan shine matsayin Atiku Abubakar yayin da yake martani ga harin da yan Boko Haram suka kai gidan gyara hali na Kuje
  • Atiku ya ce babban damuwarsa shine illar da tserewar masu laifi zai yi ga tsaron rayuka da dukiyar mutanen Abuja da kewaye

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai kan gidan gyara hali na Kuje.

Hakan ya biyo bayan harin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai gidan yarin na Kuje a daren ranar Talata wanda ya yi sanadiyar tserewar fursunoni da dama.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fallasa yan ta'addan da take zargi da kai hari Gidan Yarin Kuje

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan cewa manyan masu laifin da suka tsere daga gidan gyara halin na iya kara tabarbarar da lamarin tsaro a babbar birnin tarayya, Abuja.

Atiku
Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ya yi ikirarin cewa lamarin tsaron kasar na ci gaba da tabarbarewa saboda ‘yan Najeriya sun gaza kafa tsarin doka da oda wanda zai ba da muhimmanci ga kamawa da hukunta masu laifi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya rubuta a shafin nasa:

“Na damu kuma na yi bakin ciki da rahoton harin da wasu da ake zaton yan ta’adda ne suka kai gidan yarin Kuje. Damuwata ba wai kawai a kan yan ta’addan da ke tsare da suka gudu bane illa kan illar da ke tattare da hakan a bangaren tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja da kewaye.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

“Ina fatan sake jadadda abun da na fadi a ranar Litinin cewa gazawarmu wajen kafa wani tsari na doka da oda wanda zai ba da muhimmanci a wajen kamawa da hukunta masu laifi shine dalilin da yasa rashin tsaro ke ci gaba da habbaka a kasarmu.”

Harin gidan yarin Kuje: An girke tsauraran matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye

Mun kawo cewa an tsaurara matakan tsaro a yawancin yankuna da ke garuruwan Kuje a babbar birnin tarayya Abuja, bayan farmakin da yan bindiga suka kai cibiyar gyara hali na Kuje a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa wakilinta ya kewaye yankin inda ya tarar da jami’an tsaro dauke da manyan makamai a wurare masu muhimmanci.

NAN ta rahoto cewa an girke motocin yaki a kewayen mahadar gidan yarin na Kuje, yayin da tawagar jami’an tsaro ke ta shawagi a motocin fatrol.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel