Boko Haram sun tare motoci, sun karbe abincin da za a rabawa ‘Yan gudun hijira

Boko Haram sun tare motoci, sun karbe abincin da za a rabawa ‘Yan gudun hijira

  • ‘Yan Islamic State in West Africa Province wanda aka fi sani da ISWAP sun tare motocin abinci
  • Sojojin kungiyar ta ISWAP sun karbe abincin da aka ware domin rabawa masu gudun hijira a Borno
  • A ‘yan kwanakin nan, ‘Yan ta’adda na kokarin karbe iko da wasu garuruwa a Arewa maso gabas

Borno - Wasu daga cikin mayakan Islamic State in West Africa Province (ISWAP) sun tare motoci da ke dauke da kayan da za a ba marasa karfi a Najeriya.

Daily Trust ta ce ‘yan ta’addan sun dakile kayan abincin da za a rabawa ‘yan gudun hijira (IDPs) da mutanen da suka koma gidajensu da aka wargaza.

Kamar yadda mu ka ji labari, wannan mummunan abin ya auku ne a daren Juma’a, 8 ga watan Yuli 2022 a kauyen Layi, a karamar Mobbar a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Wani jami’in kungiyar WFP ya shaidawa jaridar cewa abincin da za a rabawa Bayin Allah a garuruwan Abadam da Mobbar ne ‘yan ta’adan suka dauke.

Sahara Reporters ta rahoto cewa majalisar dinkin Duniya tayi tanadin abinci ne ga wadanda ke gudun hijira a Abadam da mutanen da suka tare a Mobbar.

“Maharan sun zo a cikin motocin yaki hudu, bayan an yi ta gwabzawa, sun yi nasarar dakile motoci hudu, kuma sun dauke kusan duk abin da ka cikinsu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Majiya

Boko Haram
Wasu Sojojin Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana samun matsaloli

‘Yan ta’addan su na ta kai hare-hare a muhimman wurare da ke Arewa da Kudancin jihar Borno. A dalilin haka mtane ke kira ga jami’an tsaro su kara kwazo.

A yunkurin fadada daularsu, wadannan mayakan ISWAP sun shirya gudanar da sallar idi a yau a wadannan garuruwa da duk yankunan da suke hannunsu.

Kara karanta wannan

Kuje: Yadda ‘Yan ta’adda suka raba kudi, suka yi wa’azi kafin su saki ‘Yan gidan yari

Wata majiya ta tabbatar da cewa ‘yan ta’addan da ke tare da 'ya 'yan Abubakar Shekau, Abu Musab Albarnawi da Muhammad Yusuf sun dawo da karfinsu.

Duk da nasarorin da aka samu a yaki da ‘yan ta’adda, har yanzu ‘yan ta’addan Boko Haram su na yin barna jifa-jifa, su na kokarin karkato da ra’ayin jama’a.

A lokuta irin na bukukuwan sallah, ‘yan ta’addan ISWAP suke yin kira ga mutane da su shigo kungiyarsu. Ana wannan ne a Borno da masu makwabtaka da ita.

Fasa kurkukun Kuje

Ku na da labari cewa Kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP) ta dauki nauyin fasa gidan yarin Kuje da aka yi, har mutane suka sulale.

Za a ji sai da ‘yan ta’addan suka tsaya suka yi wa’azi kafin su kubutar da mutanensu daga kurkukun da ke Abuja, sannan suka raba masu kudin hawa mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel