Wata Sabuwa: Kim Jong Un Ya Kafa Sharadin Harba Makamin Nukiliya

Wata Sabuwa: Kim Jong Un Ya Kafa Sharadin Harba Makamin Nukiliya

  • Kasar Koriya ta Arewa ta sauya kundin tsarin mulkinta domin ba da damar kai harin nukiliya da zarar an an kashe shugaba Kim Jong Un
  • Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei da Amurka da Isra'ila suka yi a hare-hare
  • Bayan sauya kundin tsarin mulkin, Koriya ta Arewa ta fadi sababbin bindigogi masu dogon zango da za ta tanada a kan iyakar Koriya ta Kudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

North Korea - Koriya ta Arewa ta sauya kundin tsarin mulkinta ta yadda ya zama dole sojojinta su kaddamar da harin ramuwar gayya na nukiliya idan aka kashe Kim Jong-un.

An yi sauyin ne bayan kashe jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei da dama daga cikin manyan mashawartansa a hare-haren farko na hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a Tehran.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Gwamnatin Tinubu za ta kwaso 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu

Kim Jong Un ta nafiya a Koriya ta Arewa
Kim Jong Un da wasu sojojin Koriya ta Arewa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Nukiliya: Kim Jong Un ya sauya tsarin mulki

The Telegraph ta ce Koriya ta Arewa ta amince da gyaran tsarin mulkinta ne a zaman farko na majalisar koli ta 15, wanda aka bude a ranar 22 ga Maris 2026 a Pyongyang.

An bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026 yayin wata ganawa da manyan jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIS) ta gudanar.

A cewar bayanin NIS, Kim ne ke da ikon jagorantar rundunar nukiliyar kasar, amma sauye-sauyen sun tabbatar da hanyoyin kai harin ramuwar gayya idan aka nakasa shi ko aka kashe shi.

Sabon sashe na 3 na dokar nukiliya ya ce:

“Idan tsarin iko da jagorancin rundunar nukiliyar kasa ya shiga cikin hadari sakamakon hare-haren makiya ... za a kaddamar da harin nukiliya kai tsaye kuma nan take.”

Bayanin masani kan matakin

Kara karanta wannan

An bankaɗo girman ɓarnar da Iran ta yi wa Amurka, abin ya wuce yadda ake faɗa

Wani farfesa dan asalin Rasha a fannin tarihi da hulda tsakanin kasashe a Jami’ar Kookmin da ke Seoul, Farfesa Andrei Lankov ya ce:

“Watakila wannan manufa ta kasance tun da farko, amma yanzu an kara jaddada ta bayan an saka ta cikin kundin tsarin mulki.
“Iran ce ta zama abin misali. Koriya ta Arewa ta ga yadda hare-haren Amurka da Isra’ila suka yi tasiri cikin sauri, inda suka kashe mafi yawan shugabannin Iran nan take,”
Kim Jong Un a Koriya ta Arewa
Kim Jong Un a lokacin harba wani makami a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Magana kan iyakokin Koriya

An kule kusan gaba dayan iyakokin Koriya ta Arewa, kuma ‘ana sa ido sosai kan jami'an diflomasiyya, ma’aikatan agaji da ‘yan kasuwa daga kasashen “abokai” da ke shiga kasar.

The News Pakistan ta ce Koriya ta Arewa na shirin girke wani sabon nau’in manyan bindigogi a kan iyakarta ta kudu, wanda ka iya sanya Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu, cikin barazana.

Kim Jong Un ya harba makamai

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya harba wasu manyan makamai masu iya harbo jiragen ruwa.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Kim Jong Un ya halarci wani taro da aka yi domin harba makaman da ke nuna cewa Koriya ta Arewa tana zaune cikin shirin tunkarar duk wata barazana.

Gwaje-gwajen makaman da Koriya ta Arewa ta yi ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Iran ke cigaba da zaman doya da manja a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng