Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

  • Bolarinwa Abiodun ya damfari wani kudi har naira miliyan 266.5 bayan ya yi karyar cewa shi janar din soja ne
  • Alkalin kotun laifuka na musamman, Justis Oluwatoyin Taiwo, ya jefa Abiodun a magarkama inda zai shafe tsawon shekaru bakwai
  • Har cewa mai laifin ya yi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ambaci sunansa cikin wadanda za a nada mukamin shugaban hafsan soji

Lagos- Alkalin kotun laifuka na musamman da ke zama a Ikeja, jihar Lagas, Justis Oluwatoyin Taiwo, a ranar Alhamis, 7 ga watan Yuli ya yankewa Bolarinwa Abiodun, wani janar din soja na bogi hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

An yanke masa hukuncin ne kan tuhume-tuhume 13 da suka hada da karbar kudi ta hanyar karya, mallakar takardun bogi da kuma samun takardu na karya da ya kai N266,500,000,.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Zai Shilla Senegal Yayin Da Ake Kai Hare-Hare Da Dama a Najeriya

A wata sanarwa da hukumar EFCC ta fita, ta ce laifukan sun yi karo da sashi na 1(3) na dokar damfara da sauran laifuka masu alaka ta 2006; sashi na 363 na dokar laifuka ta jihar Lagas 2015 da sashi na 6 na dokar damfara da sauran laifuka masu alaka lamba ta 14 na 2006.

An zargin wanda ake karar, wanda hukumar EFCC reshen jihar Lagas ta gurfanar da shi a matsayin janar din rundunar sojin Najeriya da karya wajen gabatar da kansa ga mai karar, Kodef Clearing Resources, cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lissafa shi da wani mutum daya don nada su a matsayin shugaban hafsan soji, kuma cewa yana bukatar dan tallafi domin bibiyar nadin.

Janar din Bogi
Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta kuma ce an tuhumi Abiodun, wanda aka kama a gidansa da ke Alagbado na jihar Lagas a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu 2022, da kirkiran takardar nadin nasa a matsayin shugaban hafsan soji da sa hannun wai shugaban kasar sannan ya nuna ma wanda ke karar don tabbatar da ikirarinsa.

Kara karanta wannan

Valentine Day: Matashin saurayin da ya kashe budurwarsa ranar masoya zai baƙunci lahira a Jos

Asiri ya Tonu: An kama jami'an tsaro suna waya da yan ta'adda bayan harin Kuje

A wani labari na daban, mun ji cewa ana tsare da jami'an hukumar yan sanda biyu kan mummunan harin da yan ta'adda suka kai gida gyaran Halin Kuje a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'adda, waɗan da suka ci ƙarfin jami'an tsaron gidan Yarin, sun kwance Fursunoni 800, ciki har da baki ɗaya mayaƙan Boko Haram da ke tsare.

Harin wanda aka kai rana ɗaya da wani farmaki da yan bindiga suka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Katsina, ya kaɗa hanjin yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel