Masu zanga-zanga sun kusa har dakin shugaban kasa a Sri-Lanka

Masu zanga-zanga sun kusa har dakin shugaban kasa a Sri-Lanka

  • Dubban masu zanga-zanga a Sri lanka sun mamaye gidan fadar shugabankasa a Colombo don neman yayi murabus daga mukamin sa
  • Hotuna sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin ɗakin kwanan shugaban kasar inda suka rinƙa ɗaukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.
  • Mutanen kasar Sri-Lanka sun kwashe shekaru goma suna fama da matsin tattalin arziki

Matsin tattalin arziki da kasar Sri-Laka ke fama dashi na shekaru goma ya sa kuɗaɗen waje sun ƙare kuma ba a iya sayo kayayyakin amfani na yau da kullum a kasar kamar man fetur, magani da abinci ya sa hakurin mutanen kasar ya kure.

Mutanen Kasar sun jera kusan watanni hudu suna fama da wahalar bin layin neman man fetur wanda yasa makarantu ma sun shafe kusan makonni uku a rufe saboda wahalar man fetur.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'

Wannan matsin yasa dubban mutanen kasar shafe watanni suna zanga-zangar kin amincewa da yadda abubuwa ke gudana a kasar. Rahoton BBC HAUSA

SRI LANKA
Masu zanga-zanga sun kusa har dakin shugabankasa a Sri-Lanka : Foto BBC.com
Asali: AFP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sri Lanka
Masu zanga-zanga sun kusa har dakin shugabankasa a Sri-Lanka : FOTO Reuters
Asali: Getty Images

Dubban masu zanga-zanga a Sri lanka sun mamaye fadar shugaban kasar dake birnin Colombo, inda suke nemi shi dayayi murabus daga shugabancin kasar.

Hotuna a kafofin sadarwa sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin ɗakin kwanan shugaban kasar inda suka rinƙa ɗaukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.

Wasu daga cikinsu kuma sun shiga cikin wurin wanka na alfarma wato swimming pool inda suka yi ta wanka a ciki.

Bayan haka kuma wani rahoto da ya fito daga gadina talabijin na Aljazeera ya bayyana masu yan zanga-zangar sun kona gidan shugaban kasar kurmus.Rahoton Aljazeera

Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada labarin abun da yafaru

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

A wani labari kuma, Bayan harin da yan bidigan kungiyar ISWAP suka kaiwa gidan yarin Kuje a daren ranar Talata ya lafa.

Dakataccen tsohon Mataimakin kwamshinan yansanda DCP Abba Kyari wanda fursuna ne a gidan yari ya ba da labarin abin da ya auku a ranar harin, Rahton jaridar VANGUARD.

Asali: Legit.ng

Online view pixel