Harin gidan yarin Kuje: An girke tsauraran matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye

Harin gidan yarin Kuje: An girke tsauraran matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye

  • An zuba matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye a babban birnin tarayya Abuja bayan farmakin da Boko Haram suka kai gidan gyara hali na Kuje
  • Jami'an yan sanda dauke da manyan makamai sun yi wa yankunan kawanya sannan jiragensu na ta shawagi a sama
  • Hakan baya rasa nasaba da kokarin da ake yi na gano fursunonin da suka tsare da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rahotanni sun kawo cewa an tsaurara matakan tsaro a yawancin yankuna da ke garuruwan Kuje a babbar birnin tarayya Abuja, bayan farmakin da yan bindiga suka kai cibiyar gyara hali na Kuje a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa wakilinta ya kewaye yankin inda ya tarar da jami’an tsaro dauke da manyan makamai a wurare masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Gidan yarin Kuje
Harin gidan yarin Kuje: An girke tsauraran matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye Hoto: Vanguard

NAN ta rahoto cewa an girke motocin yaki a kewayen mahadar gidan yarin na Kuje, yayin da tawagar jami’an tsaro ke ta shawagi a motocin fatrol.

Yan sandan tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro; sun killace hanyoyin da zai sada mutum da yankin gidan yarin sannan an hana zirga-zirga a yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kuma gano jiragen yan sanda suna shawagi a sama yayin da bankuna da wasu makarantu suka kasance a kulle saboda tashin hankalin da ke yankin.

Sauran jami’an tsaro ma sun kasance cikin shirin ko ta kwana domin hana duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya, rahoton Vanguard.

Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewar kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje biyo bayan harin da wasu yan ta’adda suka kai a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Yuli, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

A yayin wata ziyara da ya kai cibiyar, sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Mista Shuaibu Balgore, ya yi bayanin cewa an dawo da fursunoni sama da guda 300 kuma wasu na kan hanya.

Ya kara da cewar cibiyar na dauke da fursunoni 994 kuma cewa maharan, wadanda yake zaton yan Boko Haramn ne sun farmaki cibiyar don kubutar da abokan harkarsu, rahoton PM News.

Asali: Legit.ng

Online view pixel