Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya sake samu gagarumin goyon baya kan zabin mataimaki da ya yi
  • Shugaban kungiyar CAN reshen Borno, Bishop Mohammed Naga, ya yaba ma Tinubu kan zabar tsohon gwamnan jihar, Kashim Shettima da ya yi a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa
  • Naga ya bayyana cewa al'ummar Kirista basu taba samun irin gatan da suka samu a karkashin gwamnatin Shettima ba a tarihin jihar

Borno - Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Borno, Bishop Mohammed Naga, ya yaba da zabar tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima da aka yi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya sanar da Shettima a matsayin abokin takararsa a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, duk da adawa da aka dunga nunawa kan tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

Sai dai kuma a wani yanayi da ke nuna goyon bayan takarar Shettima, kungiyar CAN reshen Borno karkashin jagorancin shugabanta ta yi maraba da wannan zabi na Tinubu, jaridar Punch ta rahoto.

Kashim Shettima
Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Bishop Naga, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, ya ce al’ummar Kirista a jihar Borno basu taba samun gata irin wanda suka samu a karkashin Shettima wanda ya yi gwamna tsakanin 2011 da 2019 ba, rahoton Thisday.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naga wanda ya bayyana Shettima a matsayin shugaba mai tausayi ya ce:

“Ba lallai bane Yan uwana wadanda ba yan jihar Borno bane su sani, amma kai da ni mun san gaskiya. A tarihin jihar Borno, babu gwamnan da ya yiwa al’ummar kirista adalci kamar yadda Gwamna Kasheim Shettima ya yi. Ina fadin wannan ne a gaban Allah madaukakin sarki kuma wannan ba komai bane face gaskiya. A tarihin Borno, Gwamna Shettima ne gwamna daya tilo da ya dauki nauyin aikin hajjin kirista mafi yawa tun 2011.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da ya dace a sani game da Kashim Shettima, abokin tafiyar Tinubu

“Ina magana ne da karfin gwiwa ba tare da tsoro ko alfarma ba saboda a matsayina na shugaban CAN bana karbar albashi ko kuma sisin kwabo daga gwamnati ko wata cibiya, amma dole a fadi gaskiya. Wannan gwamnan ya nuna tausayi ga al’ummar Kirista.
“Misali, lokacin da aka kora mutanen Gwoza daga mahaifarsu, sun tsere zuwa Maiduguri, kuma gwamnan da kansa ya zo cibiyar CAN a yankin Jerusalem sau biyu a watannin Yuni da Yulin 2014. Ya bayar da naira miliyan 10 don dawainiyarsu a karon farko, amma wadanda abun ya shafa basu da yawa. A karshen watan Oktoban 2014, yan gudun hijira daga Gwoza sun karu zuwa 42,000 a wannan sansanin kadai. Gwamna Shettima ya sake zuwa sannan ya bayar da wani naira miliyan 10. Ya kuma bayar da Karin naira miliyan 5 ga Kiristocin Borno da suka tsere zuwa Kamaru don dawo da su gida.
“Ya sake bayar da wani naira miliyan 5 ga wadanda ba yan jihar ba da suka tsere zuwa Kamaru domin su dawo Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

“Harma gwamnan ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno da ta kai abinci kai tsaye ga yan gudun hijira a karkashin shugabancin Kirista. A zahirin gaskiya, gwamnan ya nace cewa yana so yan gudun hijira Kirista su kasance a tare da takwarorinsu Musulmai a sansanonin yan gudun hijira daban-daban a nan Maiduguri amma shugabannin suka ga zai fi kyau a ware yan gudun hijira kirista don gudun fitina.
“Magana ta gaskiya a matsayina na Kirista kuma mai wa’azi, bani da wani abun jin tsoro game da daukar Musulmi da Asiwaju ya yi a matsayin abokin takararsa saboda shi ba mai zafafa addini bane kuma ina farin ciki da fadawa duniya zuciyarsa da ya yi kan mutumin da ya fi so a matsayin abokin takararsa.
“Ganin wani dan takarar shugaban kasa yana yaba masa karin martaba ne a gare shi da magoya bayan Asiwaju. Ina taya shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa masu jiran gado.”

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shettima bai san shine abokin takarata ba, in ji Tinubu

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, ya nuna gamsuwa da zabin abokin takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Asiwaju Bola Tinubu wanda ke rike da tutar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

A yayin wata hira da Arise News, Kwankwaso ya bayyana Shettima wanda ya kasance sanata mai wakiltan Borno ta taskiya a matsayin mutumin kirki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel