Ahmed Musa ya caccaki gwamnatin Buhari kan yajin aikin ASUU

Ahmed Musa ya caccaki gwamnatin Buhari kan yajin aikin ASUU

  • Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa ya yi zazzafan martani kan yajin aikin ASUU da ke gudana
  • Shahararren dan wasan kwallon kafan ya je shafinsa na soshiyal midiya don caccakar yan siyasa kan wofantar da tsarin ilimi a kasar
  • Harma ya tambayi yan siyasar da ke tura yaransu kasashen waje don yi karatu yadda suke ji alhalin yaran talakawa na gida

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya caccaki yan siyasar Najeriya kan halin ko in kula da suke nunawa a yajin aikin da malaman jami’a na ASUU ke yi.

Dan wasan kwallon kafar ya je shafinsa na Instagram a ranar Talata, 12 ga watan Yuli, don yiwa yan siyasar kasar wankin babban bargo kan tura yaransu kasashen waje domin su yi karatu yayin da tsarin ilimin kasar ke kara tabarbarewa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Yanzu dai yajin aikin ASUU ya shiga wata na biyar, sannan babu labarin komawa makarantu domin har yanzu an kasa cimma matsaya tsakanin malaman da gwamnatin tarayya.

Ahmed Musa
Ahmed Musa ya caccaki gwamnatin Buhari kan yajin aikin ASUU Hoto: @Adaeze_UC
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin dadinsa kan lamarin inda ya roki malaman jami’a da su kawo karshen yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya yi martanin ne a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli a Daura, jihar Katsina, inda ya je bikin babban sallah.

Ahmed Musa a cikin wallafar tasa ya kuma caccaki matasan Najeriya wadanda ke yabon yan siyasar duk da tsawon watanni biyar da suka shafe a gida.

Ya rubuta:

“Ga yan siyasarmu da ke rike da mukamai wadanda yaransu ke karatu a waje. Yaya kuke ji idan kuka ziyarci yaranku a kasashen waje, kuka dauki hotuna a makarantunsu sannan ku watsa a yanar gizo yayin da ASUU ke yajin aiki?

Kara karanta wannan

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

“Magana ta gaskiya, yaya hakan ya zama daidai a wajenku? Kuna tafiyar da tsarin da ku kanku baku yarda da shi ba.
“Ku nuna mun shugaban farar fata daya wanda dansa ke makaranta a Najeriya. Hakan baya taba ku?
“Sannan idan kuka dawo sai matasan Najeriya su taru suna yi maku wakar yabo.”

Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci

A wani labarin, karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kawo karshen yajin aikin malaman jami’a (ASUU) nan bada jimawa ba.

Ministan ya bayar da tabbacin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a karshen mako yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wani liyafa da abokansa suka shirya masa.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar maku cewa gwamnati ta damu sosai game da lamarin. Har yanzu da nake magana da ku tunane-tunane da dama, tattaunawa da dama da taruka na gudana da nufin magance lamarin cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Atiku: Sai da APC da su Buhari suka dawo da Najeriya baya cikin shekaru 7 kacal

Asali: Legit.ng

Online view pixel