Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla

Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla

  • Wata mata mai suna Aba ta bada labarin yadda tayi ciki tare da haifo zukeken yaro namiji ba tare da ta kwanta da namiji ba
  • A yayin tattaunawa da mai siyar da ruwa a bakin titi, ta bayyana cewa shekarunta 4 rabon da ta kwanta da namiji
  • Kwatsam cikinta ya fara kumbura tare da ciwo, koda taje asibiti sai aka ce aiki za a yi mata a ciro ciwon dake cikinta
  • Tace kawai ta ji tana son ciro abinda ke cikinta ba tare anyi mata aiki ba, lamarin da yasa tayi nishi har yaro namiji ya fado

Wata mata mai suna Aba tayi ikirarin cewa ta dauka ciki kuma ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.

Yayin zantawa da Barima Kaakyire Agyemang a step 1 TV, Aba tayi ikirarin cewa shekara hudu rabonta da kwanciya da namiji.

Kara karanta wannan

Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci

Kamar yadda tace, lokacin da ta fara fuskantar wani irin ciwon ciki da kumburi, tace tayi tunanin cutar fibroid ce.

Mace da jinjira
Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Bayan isarta asibiti, tayi ikirarin cewa an sanar da ita ta shirya za a yi mata aiki domin cire abinda ke cikinta, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta kara da cewa, ta yi kokarin yin mishi domin cutar fibroid din ta fita ba tare da an tsaga ta da wukar likita ba, amma abun mamaki sai santalelen yaro namiji ya fado.

Mahaifiyar jinjirin wacce ke siyar da ruwa a bakin titi, ta kara da cewa bata da halin kula da yaron. Ta bayyana yadda wata matar fasto ke kula da ita tare da jaririnta.

Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta

A wani labarin, an tirsasa wata matar aure ta dauka mijinta a kafadunta kuma ta zagaye titunan kauyensu bayan an kama ta dumu-dumu da wani gardi.

Kara karanta wannan

Matar Eedris Abdulkareem ta dauki nauyin ba mijinta koda

Shafin LIB ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Borpadaw aake Indiya a ranar 3 ga watan Yulin 2022.

Matar tayi batan-dabo na tsawon sati kuma mijinta da sirikanta sun dinga nemanta amma basu ganta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel