Manyan Labarai A Yau
'Yan ta'adda sun sake kai mummunan hari unguwar Keke B, Millennium City dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da mutane da yawa.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaro ta DSS sai da ta gabatar da rahotannin tsaro 44 kafin farmakin yarin Kuje.
Oluchi Mbadugha mai shekaru 29 ta gurfana a gaban kotun Majistare da ke Ogba, jihar Lagas, bayan ta yiwa matar dan uwanta, Christian Precious, dukan kawo wuka.
Bayan shafe tsawon watanni hudu a hannun yan ta’addan da suka suka yi garkuwa da su, Barista Hassan Usman, fasinjan jirgin kasan Kaduna ya sadu da yan uwansa.
Jama’a sun cika da mamaki bayan bayyanan bidiyon wani jami’in dan sandan kasar Saudiyya kuma Balarabe yana magana da Hausa tiryan-tiryan kamar wani Bakano.
Wata matashiya ta bayan ta dawo gida daga Turai ta tarar da danta cikin wani yanayi mara kyan gani. Ta ce a kullun cikin neman kudi take yi tana turawa a gida.
A wani bidiyo mai ban al'ajabi da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, an gano amarya tana sharban kuka wiwi yayin da take zaune a gefen angonta ana masu baiko
Gidauniyar Bashir Ahmad ta dauki nauyin karatun Saratu Dan-Azumi, hazikar yarinya wacce Allah ya yiwa baiwar hada lissafi duk da cewar bata zuwa makaranta.
‘Yan ta’adda na kitsa yadda za su aukawa wasu gidajen yari da ke yankin Arewacin Najeriya domin fitar da ‘yan ta’ddan da ke kurkukun Zamfara, Gusau da Katsina
Manyan Labarai A Yau
Samu kari