Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Saki, Barista Hassan Ya Sadu Da Yan Uwansa A Bidiyo

Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Saki, Barista Hassan Ya Sadu Da Yan Uwansa A Bidiyo

  • Barista Hassan Usman daya daga cikin fasinjojin jirgin kasa da yan ta'adda suka sako a yau Litinin ya hadu da yan uwansa
  • Dandazon jama'a maza da mata yan san barka sun taru don tarban Barista Usman wanda ya shaki iskar yanci
  • A jiya ne 'yan bindigan suka fitar da wani bidiyo inda suka dungi azabtar da fasinjojin da duka a cikin wani jeji

Bayan shafe tsawon watanni hudu a hannun yan ta’addan da suka yi garkuwa da su, Barista Hassan Usman ya sadu da yan uwansa.

Barista Usman dai yana daya daga cikin fashinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Yuli.

Shine wanda aka gano yana jawabi a cikin sabon bidiyon da yan ta’addan suka saki suna azabtar da su kuma yana daya daga cikin mutum uku da aka sako a yau Litinin, 25 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Bayan sake bidiyon azabtar da fasinjojin jirgin Abj-Kad, 'yan bindiga sun sako mutum 3

Fasinjan jirgin kasa da aka saki
Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Saki, Barista Hassan Ya Sadu Da Yan Uwansa A Bidiyo Hoto: diaryofanorthernwoman
Asali: Instagram

Tuni dai bawan Allan ya sadu da yan’uwa da abokan arziki wadanda suka yi tururuwan zuwa tarbansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wani bidiyo da shafin diaryofanorthernwoman ya wallafa a Instagram, an gano dandazon jama’a maza da mata sun taru yayin da baristan ya iso wajen a cikin wata mota.

Bayan fitowarsa daga motan an gano shi zaune cikin yan uwansa inda yake shakar inuwar yanci.

Harin jirgin Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako 3 cikin 62 da suka sace, suke azabtarwa

A baya mun ji cewa 'Yan ta'adda sun sako mutane uku cikin fasinjojin 62 da suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Wadanda aka sakon sun hada da maza biyu da mace daya, sun kuma samu ‘yancinsu ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa ‘yan ta’addan sun sako su ne a wani wuri da ke tsakanin dajin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Daga nan 'yan uwansu suka karbe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel