Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nuna Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce

Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nuna Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce

  • Bidiyon wata amarya tana sharban kuka wiwi tare da baran baki ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya
  • An dai gano amaryar zaune kusa da angonta cikin shiga iri daya amma sai rusa ihu take yi da hawaye
  • Koda aka je wajen rawa, sai ga yan biki sun rirrike amarya yayin da take zillewa da kokarin tserewa daga filin rawan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bisa al’ada amare kan kasance cikin farin ciki da annashuwa a duk lokacin da aka ce an taru domin saka ranar aurensu musamman idan aka yi dace da wanda suke burin karasa rayuwarsu da shi ne.

Sai dai lamarin ya sha bamban a bangaren wata amarya da bidiyonta ke yawo a shafukn soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano matashiyar budurwar tana sharban kuka wiwi yayin da take zaune a gefen angonta a lokacin da ake masu baiko.

Kara karanta wannan

Mace Mai Kamar Maza: An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

Amatya na kuka
Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nunu Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

An kuma gano wata dattijuwar mata tsaye a gabanta tana share mata hawayen da ke zuba a idanunta tare da bata hakuri yayin da ita kuma amaryar ta bare baki tana ta rusa ihu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba a nan gizo ke saka ba, sai inda aka nuno jama’a sun taru suna rawa amma ita amaryar tana ci gaba da kuka tare da zillewa. Sai kuma ga mutane sun rirrike ta don gudun kada ta tsere daga wajen.

Wannan al’amari ya baiwa mutane da dama mamaki, inda wasu ke tunanin kodai auren dole ake shirin yi mata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

value_active ta yi martani:

“Ah ah wani irin wahala ne wannan wai dole ne”

suomanuunyango ta ce:

“Wannan abun bakin ciki ne. Mai motsa zuciya.”

pheedybukar ta ce:

Kara karanta wannan

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

“Wannan kamar yarinya ce kawai Wallahi ”

ayysherh_maikano__ ta yi martani:

“Wai dole ne”

real_beebahbeeyou

“Ko shakka babu gobe ta sa masa guba, za su ce ta kashe mutum yayin da karara ya ga cewa baya farin ciki. Wasu mazan ma dai ban san masu ba.”

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

A wani labarin, Hausawa kan ce aure shine babban yakin mata domin za su bar iyaye, yan uwa da danginsu sannan su koma rayuwa cikin wasu sabbin mutane da basu sani ba.

Wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya na wata amarya da ta fashe da kuka a wajen liyafar bikinta.

A cikin bidiyon wanda shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano amaryar tsaye rike da hannayen mahaifiyarta a filin rawa inda mai gabatar da shirin ta bukaci da ta fadawa mahaifiyarta tana kaunarta kuma za ta yi kewanta.

Kara karanta wannan

Matashi ya caccaki 'yan mata, ya ce duk budurwar da bata tashi bacci har 8, to malalaciya ce

Asali: Legit.ng

Online view pixel