Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

  • Cike da rauni, wata matashiya da ke zaune a kasar waje ta koka da ganin yanayin da danta yake ciki
  • Kamar yadda ta bayyana, ta mayar da hankali sosai wajen neman kudi tare da aikawa gida don a kula shi
  • Ga mamakinta, ta yi dawowar bazata kawai sai ta tsince shi a wani irin yanayi mai ban tausayi

Wata matashiya ta koka a shafin soshiyal midiya bayan ta dawo gida daga Turai ta tarar da danta cikin wani yanayi mara kyan gani.

Da take wallafa bidiyon yaron a shafinta na TikTok mai suna @.its_me_honey, matashiyar ta rubuta cewa tana aiki tukuru a kasar waje.

Uwa da da
Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo Hoto: TikTok/@.its_me_honey
Asali: UGC

Ta kara da cewar ta tura dukka kudadenta gida don a kula mata da yaron yadda ya kamata, don haka yanayin da ta riske shi ya raunana mata zuciya.

Kara karanta wannan

Cin Amana: Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

Alamu sun nuna ta dawo kasar ne ba tare da sanin kowa ba. Ta yada hotunan da ta dauka tare da yaron a wannan yanayi. Bidiyon na dauke da rubutu kamar haka:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kana aiki tukuru tare da tura dukka kudadenka gida amma sai kawai ka riski danka a wannan yanayi.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Sheilla nash ta ce:

“Kada ki damu yar’uwa fi muhimmanci shine cewa ya yana cikin farin ciki da rai...kawai ki kalli farin cikin da ke fuskarsa. Ki fara Daga nan sannan ki gode na Allah cewa yana da rai.”

Sunshine ya ce:

“Babu dadi amma yana da rai. Ki fara daga farko, ki bashi kulawar da kike so ya samu. Lokaci bai kure ba.”

Helena clairs ta ce:

“Na san yadda kike ji yan mata amma akalla naki da kyau nawa kashi kawai ya rage kawai Ina jira ne ta rubuta jarrabawar js3 dinta.”

Kara karanta wannan

Mace Mai Kamar Maza: An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

sinachbinyosh ta ce:

“Kada ki damu yar’uwa idan yana da rai da lafiya ki gode Allah nawa dan ya mutu na bar kasar shekaru uku yanzu kawai sai dawowa nayi na ziyarci kabarin dana.”

Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nuna Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labari na daban, bisa al’ada amare kan kasance cikin farin ciki da annashuwa a duk lokacin da aka ce an taru domin saka ranar aurensu musamman idan aka yi dace da wanda suke burin karasa rayuwarsu da shi ne.

Sai dai lamarin ya sha bamban a bangaren wata amarya da bidiyonta ke yawo a shafukn soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano matashiyar budurwar tana sharban kuka wiwi yayin da take zaune a gefen angonta a lokacin da ake masu baiko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel