DSS Sai Da Ta Gabatar Da rahotannin tsaro 44 Kafin Harin Kuje, In Ji Wase

DSS Sai Da Ta Gabatar Da rahotannin tsaro 44 Kafin Harin Kuje, In Ji Wase

  • Sabon bayanai da ke fitowa sun nuna hukumar tsaro ta DSS ta gabatar da rahotanni kafin farmakin magarkamar Kuje
  • Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya tabbatar da cewar DSS ta gabatar da rahotanni 44 kafin yan ta'addan suka kaddamar da harin
  • Babbar birnin tarayya Abuja dai na fama da yawan hare-haren yan bindiga a baya-bayan nan, sun kuma yi barazanar sace Shugaba Muhammadu Buhari

Abuja - Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta gabatar da rahotannin tsaro 44 kafin farmakin da yan bindiga suka kai magarkamar Kuje, Daily Trust ta rahoto.

A ranar 25 ga watan Yuli ne yan ta’adda suka farmaki gidan yarin na Kuje sannan suka saki fiye da fursunoni 800 ciki harda dukkanin yan Boko Haram da ke tsare.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

Idris Wase
DSS Sai Da Ta Gabatar Da rahotannin tsaro 44 Kafin Harin Kuje, In Ji Wase Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wase ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da gudunmawarsa a kan kudirin dakatar da shirin haramta amfani da babura a fadin kasar da gwamnatin tarayya ke kokarin yi.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duba irin abun da ke faruwa a Abuja a yau. Zan fada maku gaskiya. Na yi nazarin rahotannin DSS. Rahotanni 44 aka bayar kafin harin Kuje. Ina son cewa, ina mai tabbatar maku, 44. Na bibiyi dukkanin rahotannin. Kuma duk yana da alaka da wannan.
“Babu wani gari da hari zai faru da ba za mu samu bayanan sirri ba, kuma wannan yana daga cikin bayan sirrin da suka bayar kana abun da zai faru. Abun da yake faruwa da kuma abun da ba zai faru ba.”

Sai dai kuma, Wase ya ce ya kamata a tallafa wa gwamnati don aiwatar da irin wannan yunkuri a cikin garuruwa masu rauni inda dokar za ta iya tasiri kan fashi da makami, ta'addanci da sauran laifuka, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jihar arewa, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata

Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

A baya mun kawo cewa Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta amfani da babura wanda aka fi sani da Okada a fadin kasar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ne ya yi tsokacin yayin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar tsaro ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Malami ya ce bincike ya nuna cewa amfani da babura wajen gudanar da ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasar nan kuma sanya haramcin na iya katse hanyoyin samun kudaden yan ta’adda da yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel