Bidiyon Yadda Wani Jami’in Tsaro Balarabe Ke Zuba Hausa Kamar Jakin-Kano A Saudiyya
- An jiyo jami'in tsaron na Saudiya wanda ya kasance Balarabe yana magana da harshen Hausa tiryan-tiryan kamar wani Bahaushen usuli
- Ahmad wanda yace sunansa na Najeriya 'manya-manya maganin kanana' ya ce Allah ne ya nufa zai ji harshen na Hausa
- Wannan al'amari ya burge mutane da dama inda suka ce ya yi kokari, wasu kuma sun ce ya yi kamar Bakano
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jama’a sun cika da mamaki bayan bayyana bidiyon wani jami’in dan sandan kasar Saudiyya kuma Balarabe yana Hausa tiryan-tiryan kamar wani Bakano.
A cikin bidiyon wanda shafin _garkuwanarewa ya wallafa a Instagram, an jiwo wani Bahaushe yana yi masa tambayoyi kan yadda aka yi ya iya Hausa haka.
Sai dai kuma, Balaraben wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ahmad ya ce mahaifiyarsa ta haife sa ne a cikin Hausawa.
Ya kuma bayyana cewa sunansa na Najeriya ‘Manya Manya maganin kanana’.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai mutumin ya so ci gaba da yi masa tambayoyi inda ya bayyana cewa aiki sun yi masa yawa sosai bai da lokacin amsawa.
Ga yadda hirar tasu ta kaya
Bahaushen ya tambaye shi yaya sunan sa sai Balaraben yace:
“Sunana na nan ko na Najeriya? Sunana na Najeriya ‘manya manya maganin kanana’ amma sunana na nan Ahmad."
Sai Bahaushen ya tambaye shi yaya aka yi ka ji Hausa, sai ya amsa masa da:
“Ka tambayi Allah, domin Allah ne ya bani. Mamata ta haife ni cikin mutanenku."
Da aka tambaye shi a wani unguwa yake sai yace:
“Na nan ko na Najeriya. Na nan Makkah.”
Kalli cikakken bidiyon a kasa:
Martanin mutane kan bidiyon
comrade_bbs1 ya yi martani:
"MashAllah."
thefarouuq ya ce:
"Kuma hausar tashi kamar Bakano ❤️"
afrahs_collections ta ce:
"Yace aiki ya bani yawagadkiya yayi kokari fa"
Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo
A wani labarin, wata matashiya ta koka a shafin soshiyal midiya bayan ta dawo gida daga Turai ta tarar da danta cikin wani yanayi mara kyan gani.
Da take wallafa bidiyon yaron a shafinta na TikTok mai suna @.its_me_honey, matashiyar ta rubuta cewa tana aiki tukuru a kasar waje.
Ta kara da cewar ta tura dukka kudadenta gida don a kula mata da yaron yadda ya kamata, don haka yanayin da ta riske shi ya raunana mata zuciya.
Asali: Legit.ng