Zafafan Hotunan Shugaban Bankin AfDB Da Zukekiyar Matarsa Yayin Da Suka Cika Shekaru 38 Da Aure

Zafafan Hotunan Shugaban Bankin AfDB Da Zukekiyar Matarsa Yayin Da Suka Cika Shekaru 38 Da Aure

  • Soyayya bata tsufa sai dai ma'abota yinta su tsufa in ji masu hikimar zance
  • Shugaban Bankin Cigaban Nahiyar Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina, da matarsa, Grace, sun cika shekaru 38 da shiga daga ciki
  • Hadaddun hotunansu sun bayyana yayin da suke raya wannan rana, inda tsohon ministan na Najeriya ya budewa matar tasa sirrin zuciyarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban Bankin Cigaban Nahiyar Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina, da matarsa, Grace, sun yi bikin cikarsu shekaru 38 da yin aure.

Adesina wanda ya kasance tsohon ministan noma da raya karkara na Najeriya, ya wallafa hotunansu domin raya wannan rana a shafinsa na Twitter.

Adesina da matarsa
Zafafan Hotunan Shugaban Bankin AfDB Da Matarsa Yayin Da Suka Cika Shekaru 38 Da Aure Hoto: @akin_adesina
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana matar tasa a matsayin babban kyauta da Allah ya yi masa a rayuwa, inda ya furta wasu zantuka masu ratsa zukatan masoya.

Ya rubuta a shafin nasa:

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya Sauka Daga mulki, ko a Tsige shi Inji Jam’iyyar NNPP

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Masoyiyata, Grace: Yayin da muke murnar cikarmu shekaru 38 da aure a yau, ina kaunarki a yau fiye da kullun. Kece babbar kyauta da ni’imar Allah a gareni. Kina da kyau, kulawa, kirki da tsoron Allah- mata abin koyi, uwa kuma babbar aminiyata. Barka da zagayowar shekara masoyiya! Ina kaunarki!”

Ku Hana Su 'Yan Matanku Fitar Da Tsiraici Ranar Aurenku, Fasto Ya Shawarci Amaren Da Zasu Shiga Daga Ciki

A wani labarin kuma, shahararren fasto, Agyeman Elvis ya shawarci amaren da ke shirin shiga daga ciki a kan su yi taka-tsan-tsan da irin kawayen da suke zaba a matsayin yan matan amarya.

Fasto Agyemang Elvis a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa akwai wasu yan mata da ke nuna tsaraicinsu duk don su ja hankalin ango zuwa kansu.

Kara karanta wannan

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

Sannan ya ce manufar wasu kuma shine kure adaka don kawai su nunawa duniya cewa sun fi amaryar kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel